Matar da ta kirkiri 'Mammy Market' a barikin sojoji ta mutu ta na da shekaru 86
Matar da ta kafa Kasuwar Mammy Market da a barikin sojoji a fadin kasar nan, Maria Ochefu, ta mutu.
Ɗan ta, Farfesa Yakubu Ochefu, wanda ya zanta da wakilin Punch ta wayar tarho a a yau Alhamis, ya ce ta mutu ne a cikin barcin da take yi a ranar Talata.
Mai shekaru 86, ta auri Kanar Anthony Ochefu, wanda ya taba zama gwamnan soji a jihar Enugu.
A wata hira ta karshe da ta yi da jaridar PUNCH a shekarun baya, Ochefu ta bayyana yadda ta fara Kasuwar Mammy, wadda daga baya ta zama hantsi leka gidan kowa a duk barikin sojoji da ke fadin kasar nan.
A yayin tattaunawar, ta ambaci wasu shugabannin kasa guda biyu da suka shude, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, duk sun yi ritaya a matsayin kwastomominta.
Ochefu ya ce, “Eh, Mama ta rasu ranar Talata a Makurdi tana tsaka da barci," in ji ɗan nata.
managarciya