Matakan da gwamnati ke dauka kan tsaro ya taimaka a habbakar kasuwancin kayan gwari----Shugaban Kasuwa

Babban sakataren wanda hakama shine ya wakilci shugaban kungiyar na kasuwar Mile 12 dake Lagos, ya kara da cewa sukan zauna su rubuta korafe-korafen da aka gabatar masu tare da komawa dasu domin tattaunawa ta musamman a tsakanin shuwagabannin kasuwar ta Mile 12 domin yin duk mai yuwa wajen dinke wannan korafin da ‘yan kasuwar suka gabatar masu. Shugaban kasuwar wanda ya maganta a tabakin sakataren kasuwar Alh Idris Balarabe yace sam matsalar tsaro ta daina shafuwar kasuwancin da suke gudanarwa, idan aka kwatanta da lokacin baya da matsalar ta mamaye kusan dukkanin jihohin da ake noma kayan gwarin a jihohin arewa.

Matakan da gwamnati ke dauka kan tsaro ya taimaka a habbakar kasuwancin kayan gwari----Shugaban Kasuwa
 
Daga Aminu Amanawa, Sokoto.
 
Shugaban kasuwar kayan gwari ta kasa da kasa ta Mile 12 dake Lagos Alhaji  Shehu Usman Jibril, ya bayyana cewa matakan da gwamnati ke dauka na inganta lamurran tsaro a Nijeriya ya taimaka wa lamurran kasuwancin kayan gwari, musamman na iya safarar su daga jihohin arewa dake fama da matsalar tasaro zuwa kasuwar kayan gwari ta Mile 12.
Shugaban na bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara da jagororin kasuwar ke gudanarwa a duk shekara domin tattauna nasarori da irin kalubalen da masu noma da kasuwancin kayan gwarin ke fuskanta, taron da a wannan shekarar ya gudana a jihar Sakkwato.
 “Mun shirya wannan taron ne domin fahimtar juna, tsakanin masu noma da safarar kayan gwari dama mu da ake kaiwa kayan, dama yin nazari kan irin nasarori da kalubalen da sana’ar tamu ke fuskanta domin yin gyara inda ke bukatar gyaran, la’akari da irin kokari da kasuwar keyi wajen samar da ayukkan yi ga dubban jama’a a jihar Lagos inji shi”.
Babban sakataren wanda hakama shine ya wakilci shugaban kungiyar na kasuwar Mile 12 dake Lagos, ya kara da cewa sukan zauna su rubuta korafe-korafen da aka gabatar masu tare da komawa dasu domin tattaunawa ta musamman a tsakanin shuwagabannin kasuwar ta Mile 12 domin yin duk mai yuwa wajen dinke wannan korafin da ‘yan kasuwar suka gabatar masu.
Shugaban kasuwar wanda ya maganta a tabakin sakataren kasuwar Alh Idris Balarabe yace sam matsalar tsaro ta daina shafuwar kasuwancin da suke gudanarwa, idan aka kwatanta da lokacin baya da matsalar ta mamaye kusan dukkanin jihohin da ake noma kayan gwarin a jihohin arewa.
“Kaga a Maiduguri an samu matsalar Boko Haram, matsalar data hana su yin noma da sauran kayayyaki irin busashen tattasai da kifi da ake kaiwa duka abun ya tsaya saboda matsalar nan ta tsaro, to amma a baya-bayyanan an samu cigaba, idan kaduba a kasuwar Damasak zaka ga ana cin kasuwa, kuma kaga suna noma da sauran su, hakama arewa maso yamma gwamnonin na kokari ta bangaren tsaro, sukan nemi gwamnatin tarayya, ita kuma ta tura dakarun ta domin kai farmaki ga wadannan ‘yan ta’addan.”.
Bisa wannan ne shugaban yayi kira ga ‘yan kasuwa dasu rika sanya tsoron Allah a dukkanin lamurran kasuwancin da suke gudanarwa, 
Shima da yake magantawa shugaban kungiyar masu noma da kasuwancin albasa na kasa Aliyu Mai Ta Samu Isa, wanda mataimakin sa Dr Mansur Muhammad Aleru, ya bayyana jin dadinsa kan zabar Sakkwato domin gudanar da taron, la’akari da irin muhimmancin da jihar Sokoto keda wajen noma dama fiton kayan gwarin da ake samarwa.
Kamar yanda ‘yan kasuwar Mile 12 suka dauke mu da muhimmanci, muma haka muka dauke su da muhimmanci, kuma zamu cigaba da basu goyon bayan duk da suke bukata domin samun nasarar kasuwancin namu a cewar shugaban.
Taron da ya cirato mahalartan sa da suka hadar manoma, ‘yan kasuwa, dama shuwagabannin rassan kayan gwarin, ya sanya Aliyu Muhammad Tsagau dake zamowa shugaban manoma da kasuwancin Karas na jihar Sakkwato bayyana irin tarin nasarorin da suka sama duk kuwa da tarin kalubalen dake ci masu tuwo a kwarya.
“Daya daga tarin nasarorin da muka samu shine, samun hadin kan al’umma domin fahimtar abinda jagorori suka zowa manoma da masu kasuwancin albasar dashi.
Jihar Sokoto dai na daga cikin jihohin da sukayi fice a najeriya, wajen noma kayan gwari irin su Albasa, Karas, Latas, Kokunba, Tattasai, Tarugu, Yalo, Tumatir da sauran kayan gwarin amfanin yau da kullum.