Mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato Honarabul Manir Muhammad Dan’iya ya bar jam’iyarsa ta PDP.
Barin jam’iyar ya fito a wata takardar da ya sanyawa hannu dake yawo a kafafen sadarwa na zamani wadda ya aika ga shugaban mazabarsa ta Kware a karamar hukumar Kware a jihar Sakkwato.
A takardar Mataimakin Gwamna ya sanar cewa ya janye shedar zamansa dan jam’iyar PDP tun da 8 ga watan Fabarairu na 2023.
Ya godewa damar da aka ba shi ya yi aiki matakai da dama a cikin jam’iyar PDP.
Darakta yada labarai a ofishin mataimakin gwamnan Aminu Abdullahi bai dauki wayarmu ba domin sanin sahihancin takardar.





