Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto Honarabul Manir Muhammad Dan'iya, ya Saye Form na bayyana aniyarsa ta takarar Gwamnan Jihar Sokoto a Zaben kasa na 2023 cikin jam'iyar PDP zuwa yanzu shi ne mutum na hudu.
Alhaji Murtala Dan’iya tare da Rakiyar Usman El-Kudan da Barista Adah ne suka amso masa form din a Ofishin Uwar Jamiyar PDP dake Abuja.
Mataimakin Gwamnan ya yi godiya ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal akan dama da ya bashi na taya shi jagorancin Jihar Sokoto, kuma yana neman Adduoi da samun nasara a sabuwar tafiya.