Mata Na Baya Wajen Samun Madafun Iko A Nijeriya---Hukuma

Mata Na Baya Wajen Samun Madafun Iko A Nijeriya---Hukuma

 

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, NBS, ta baiyana cewa har yanzu an bar mata a baya a Nijeriya wajen samun madafun iko, idan a ka kwatanta su da maza a ƙasar.

 
Wannan na ƙunshe ne a wani rahoto da ya fito a yau Lahadi a Abuja daga Kundin Ƙididdigar Jinsi na Watanni uku-uku, na wata ukun farko a 2022.
 
Kundin rahoton ya maida hankali ne a kan wasu lamura uku da su ka haɗa da, mulki, madafar iko, lafiya, ƙididdigar al'umma da kuma ilimi.
 
A cewar rahoton, ƙididdiga ta nuna cewa kashi mata da su ke fito wa a matsayin abokan takarar shugabancin ƙasa da ga 2019 zuwa 2022 kashi 0 ne cikin 100,  yayin da na maza kuma 100 ne bisa 100.
 
Rahoton ya ƙara da cewa adadin mata 6 ne su ka tsaya takarar shugaban ƙasa a 2019, inda maza kuma 67 ne.
 
Sai kuma ya kara da baiyana cewa adadin mata 26 ne su ka tsaya a matsayin abokan takara, a maimakon 52 daga ɓangaren maza. 
 
Hakazalika, rahoton ya ce mata 80 ne su ka fito takararar gwamna a zaɓen 2019, inda maza kuma su  984 ne, inda mata 271 su ka zama abokan takarar gwamna, su kuma maza su 789 ne. 
 
Rahotannin ya kuma yi nuni s ɓangarori da dama da muƙaman maza su ka ninninka na mata a faɗin ƙasar nan.