Mata Masu Zanga-Zanga Sun Huce Haushi Da Gidan Hakimin Bokkos
Wasu mata da suka gudanar da zanga-zanga sun kona gidan hakimin karamar hukumar Bokkos Monday Adanchin ranar Alhamis.
Wani mazaunin Bokkos da baya so a fadi sunnan sa saboda tsaro ya ce matan sun kona gidan hakimin ne domin nuna adawar su da yadda sojoji suka kama wasu matasa dangane da kisan wani Bafulatani da aka yi a karamar hukumar ranar Alhamis.
Wakilin PREMIUM TIMES ya samu labarin haka ne yayin da majiyan ya kai shi gidan hakimin Ruwi, Nicolas Random domin tattauna kisan gillan da ‘yan bindiga suka yi a kauyukan karamar hukumar ranar jajibirin Kirismati.
“A ranar Alhamis ne aka kashe wani Bafulatani makiyayi a New Layout inda hakan ya sa sojoji suka kama wasu matasa da suke zargin suna da hannu a aka kai su garin Jos.
“Matan sun nemi a yi gaggawar sako wadannan matasa domin a ra’ayinsu basu aikata laifin komai ba.
Random shima ya tabbatar da haka inda ya ke cewa za shi Bokkos domin tabbatar da abin da ya faru.
Wani majiyan ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES cewa Bafulatanin da aka kashe mazaunin kauyen Hurki ne sannan an kashe shi a Kasuwan Awaki ranar Alhamis.
Ya ce sojoji sun kama matasa 8 dangane da kisan.
Bayan haka a ranar Laraban da ya gabata ‘yan bindiga sun kashe limami a kauyen Dung Sani Idris sannan suka harbe kanensa Aliyu duk a Bokkos.
Aliyu na wani asibiti mai zaman kansa likitoci na duba shi.
managarciya