Mata Masu Juna Biyu Sun Koka Kan Karancin Ma'aikatan Lafiya a Neja

Mata Masu Juna Biyu Sun Koka Kan Karancin Ma'aikatan Lafiya a Neja

 

Mata masu Juna biyu sun koka kan Karancin Ma'aikatan lafiya da likitoci a asibitin Mata ta Babangida a  jihar Neja.

A lokacin da manema labarai suka zoyarci asibitin sun samu mata sama 300 ayashe suna jiran likita ya duba su kan juna biyunsu ga shi likita daya ne ke duba su a wurina.

An samu bayanin daruruwan mata ne ke bukatar ganin likita a duk rana Amma asibitin likita shidda ne gare su.
Daya daga cikin matan ta ce da yawansu suna zuwa asibiti tun karfe 5 na asuba amma sai su koma gida ba a duba su ba domin karancin likitoci.