Home Labarai Masunta sun karya dokar  kamun kifi ta Argungu

Masunta sun karya dokar  kamun kifi ta Argungu

4
0

Masunta sun karya dokar kamun kifi wanda aka shirya a Argungu.

Masunta sun gaji da jiran shugaban kasa Bola Tinubu sun shiga ruwa don kamun kifi na tare da an basu umarni ba.

Dokar kamun kifin dole ne sai shugaban ƙasa ya zo, Sannan a hura usur sai masunta su shiga cikin ruwan don kamun kifi.

Yusuf Muhammad ya ce wannan rashin ɗa’a ne masunta suka yi a wannan shekarar, sun sani ba a shiga ruwa sai shugaban kasa ya zo, don haka duk wanda ya kama kifi ba ya cikin gasa ba za a yi lissafi da shi ba don ya yi rashin ɗa’a.

“Mun ba da minti biyar duk wanda bai fita ba za a fashe gorarsa, kowa ya fita a jira shugabanni.”

“Sarkin ruwa ya riƙe manyan kifaye ba za a iya ganinsu ba,” a cewar sa wanda yana cikin jagorori a bukin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here