Masu rajin haɗa maja don kada APC na yin hakan ne don ba su samu muƙami ba - Masari

Aminu Masari, tsohon gwamnan jihar Katsina, ya ce babu wata madafa a Nijeriya sama da jam’iyyar APC.
Masari ya yi wannan jawabi ne a jiya Lahadi a garin Kafur, karamar hukumar Kafur ta Katsina, yayin kaddamar da yakin neman zaben ƙananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga watan Fabrairu.
Tsohon gwamnan ya yi watsi da labarin ‘yan siyasa masu shirin kafa jam'iyyar maja domin kawar da jam’iyyar APC mai mulki, yana mai bayyana hakan a matsayin gungun wasu fusatattu da su ka rasa muƙamai a cikin jam’iyyar.
“Labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa wasu ‘yan siyasa na nan na hada kai don kafa maja ba komai ba ne illa taron wasu fusatattu da su ka rasa muƙamai a jam’iyyar APC,” in ji Masari.
"Yunkurin nasu na kulla kawance ba zai kawar da hankalin APC daga tunani aiwatar da ayyukan ci gaba da za su rage radadin talaka ba,".
Masari ya ce a matsayinsa na wanda da shi aka kafa jam’iyyar APC, zai ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da manufofin jam’iyyar.