Masu Fada Aji A Zamfara Ne Ke Tallafawa 'Yan Bindiga---Bello Matawalle
Gwamnan jihar Zamfara Belllo Muhammad Matawalle ya bayyana cewa yana da wasu kwararrun hujjoji da sukaa nuna manya masu fada aji a jihar na cikin wadanda ke taimakawa ayukkan ta'addanci a jihar.
Cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamna Matawalle shawara kan harkakokin yada labarai Malam Zailani Bappa ya fitar, yace hakan ne ya sa gwamna Bello Matawalle yakan yi rantsuwa da kur’ani mai tsarki, ya kuma bukaci wadanda ke cikin gwamnatina da su yi hakan, domin nisantar da kansu daga ayyukan ’yan bindiga a jihar.
Gwamna ya kuma yi kira ga duk ’yan jihar da shugabannin siyasa da su bi sahunmu domin tsabtace kansu daga duk wani zargi na mu’amala da ’yan ta’adda.
“Ba sa son ’ya’yanmu su je makaranta, ba sa son mu yi tafiye-tafiye mu samu abin dogaro da kai, ba sa son mu samu zaman lafiya a gidajenmu da garuruwa da kauyukanmu, suna son mutane su yi tawaye ga gwamnatin jiha da ta tarayya. Amma ba za su yi nasara ba. Nasarar ta mu ce da yardar Allah Madaukakin Sarki”.
managarciya