Masari Ya Jagoranci Dattawan Katsina Wurin Buhari Kan Matsalar Tsaron Jihar

Masari Ya Jagoranci Dattawan Katsina Wurin Buhari Kan Matsalar Tsaron Jihar
Masari Ya Jagoranci Dattawan Katsina Wurin Buhari Kan Matsalar Tsaron Jihar
Dattawan Jihar Katsina Sun Ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan matsalar da jihar ke fuskanta akan sha'anin tsaro.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tawagar Dattawan Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Honarabul  Aminu Bello Masari a fadar Gwamnatin Najeriya dake Abuja ranar Talata.
Tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari akwai shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari, Alh. Aliyu Mohammed, Dr. Osagie Ehanire Ministan lafiya, Ministan harkokin Jiragen sama Sanata Hadi Sirika, yayin da Shugaban  ya amshi bakuncin tawagar Dattawan na Jihar Katsina.
Gwamnan Jihar Katsina shi ne ya Jagoranci tawagar Dattawan zuwa fadar Shugaban kasar don ganawa da Shugaba kasar, tawagar Dattawan na Jihar Katsina sun hada da, Alhaji Nalado Sarkin/Sudan, Senator Mamman Abubakar Danmusa, Sanata Abba Ali, Alhaji  Ahmed Yusuf, Alhaji Ali Sani.
Gwamna Masari ya miƙawa shugaban ƙasa takardar koken jihar da hanyoyin da suke ganin yakamata a bi kan daƙile matsalar a yankin nasu.