Manyan Jam’iyyun Siyasa a Jihar Adamawa Na Cikin Tsaka Mai Wuya a Yunƙurinsu Na Lashe Zaɓen Gwamna

Manyan Jam’iyyun Siyasa a Jihar Adamawa Na Cikin Tsaka Mai Wuya a Yunƙurinsu Na Lashe Zaɓen Gwamna

Daga Aisha Aliyu Mubi.

Da aka kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar, sai ga sauye-sauyen siyasa sun zama ruwan dare. Wadannan yunƙurin sun bayyana a cikin sauye-sauyen da aka yi da sababbin 'yan takara da abokan takara.

Tun da aka fara tunkarar zaben 2023 jam’iyya mai mulki a jihar, (PDP) tana cikin tsaka mai wuya. Dan takarar jam’iyyar wanda shine gwamna mai ci, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya zabi mataimakin shugaban jami’ar jihar Adamawa (ADSU), Farfesa Kaleptapwa Farauta, a matsayin abokiiyar  takararsa a zaben gwamna na 2023. Inda wasu na ganin kamar hakan dabarar yaki ne a siyasance

Mace da gwamnan ya zaba Farfesa Farauta wadda ta fito daga Numan  ta kasance mataimakiyar shugabar kungiyar ta ADSU tun a watan Fabrairun 2020. Ta taba rike mukamin shugabar hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Adamawa sannan ta zama kwamishiniyar ilimi.

Sai kuma sanata Aisha dahiru binnai itace 'yar takarar gwamna a Kardashin jam'iyyar Apc wanda ta samu dubban goyon bayan mata a jihar, 

Sai dai wasu maluman addinin musulinci na taka mata biriki saboda a cewar su mace a matsayin shugaba haramun ne a ddainin islama, inda take samun cikas wurin zamar ta gwamna.