Managarciya Na Neman Marubuta

Managarciya Na Neman Marubuta
Amadadin hukumar gudanarwa ta kafar yada labarai mai suna MANAGARCIYA na bukatar gudunmuwar marubuta domin kara ciyar da al’umma a gaba.
Managarciya na bukatar rubutun makala kan wani maudu’i da marubuci ya zaba domin ilmanatarwa da fadakarwa a cikin al’umma.
A duk makala daya akwai dan hasafi na naira 1000 don sanya kati da za a baiwa marubuci bayan cika sharudda kamar haka:
- Sai mutum 500 sun bude makalar marubuci,
- Sai an samu share 20 na makalar,
- Ana bukatar Comment 20 na mutane daban-daban,
- Sai an samu like na mutum 10 a makalar.
Duk marubucin da ya aminta da hakan zai iya turo makalarsa ta wannan adireshi: managarciya@gmail.com zai kuma turo email da za a yi masa rijista a saman web na Managarciya domin bibiyar sakamakon sharudda da wallafa wasu rubutu da yake bukata.
Mun gode,
Edita.