MAMAYA:Labarin Soyayya Mai Ban Al'ajabi Tsakanin Mutum Da Aljan, Fita Ta Uku

MAMAYA:Labarin Soyayya Mai Ban Al'ajabi Tsakanin Mutum Da Aljan, Fita Ta Uku

*Shafi na ukku*

 

 

Tun da Bilkisu ta fice zuwa makaranta sai Inna ta samu natsuwa ta jita wasai tamkar ba abin da ke damunta , ta manta da maganar wani guntun mutum .

 

 

Bilkisu na shiga class ɗinsu kai tsaye kujerar zamansu ta tunkara kanta a ƙasa , "Ke ,, kalmar data ratsa kunnenta kenan cikin ƙaraji da amsa kuwa , cak ta tsaya inda take cikin tashin hankali domin ta yi zaton ta tsallake rijiya da baya tun da ta baro filin taren lattin.

"Ke ba magana nake maki ba ?

 

Cike da tsoro ta ɗago kanta dan ganin wane malami ne wannan muryaisa tamkar ta an tada inji (Gen)saboda amsa kuwarta da amonta.

 

Ido huɗu sukai da malamin daya tsaida ta waje ,wannan karon hatta kayan jikinsa basu bane jikinsa data ganshi dasu a filin taren Lattin ba idan har idanunta sun faɗa mata gaskiya ,

A hankali ta koma da baya ta tunkari gaban class ɗin inda yake tsaye da fuskar shanu , ko kaɗan ba fara'a a fuskarsa ,kai da ganinsa kasan na musamman ne cikin jerin malamai marassa wasa da aikinsu .

 

Tsikar jikinta kawai ke tashi zuciyarta na dukan luguden tara_tara , amma zuciyarta bata sarara da ambaton Allah ba, "ya ilahi , hasbinallahu wani'imalwakin ,,

 

Ahankali ta fara jin saukar natsuwa a zuciyarta da dukkan sassan jikinta  ,

 

Gaba ɗaya ƴan class ɗin sai suka natsu suna ganin abin tamkar wani sabon lamari ne wanda basu taɓa ganin faruwar sa a cikin class dinba .

 

Kasancewar kowa yasan dokar malaman makarantar in dai ka makara to bazaka shiga cikin class ai darasin farko da kaiba sai dai kaje ka wanke banɗakunan makarantar.

 

Kai tsaye Bilkisu gun fanfo ta nufa da nufin tarai ruwan da zatai amfani dasu gun wanke banɗakin .

 

Kasancewar fanfunan ruwan makarantar nesa kaɗan da inda classes dinsu suke sai daga can gefe aka kewaye masu banɗakunan su a gefe wajen da babu komi illa itatuwa da tarin bolai makarantar tasu .

 

Tun daga nesa ta hango fanfo ɗaya kunne yana ta zuba cike da tsoro ta ƙara duban fanfon , jini ne ke zubuwa madadin ruwa hadda gullama_gullama na  gudan jinin ke zubuwa .

Kusan suman tsaye tayi inda take , a hankali ta fara ɗaga kafafunta da niyyar komawa baya , amma kash !

Wani siririn yatsane yai fitar burgun daga cikin fanfon dake kusa da ruwan jinin.

 

Bata ankaraba taji ya cukuikuyeta yana jawota baya da karfin tsiya .

 

Cike da tashin hankali ta fara ƙoƙarin kwace hijabinta ta ruga amma ina tamkar wani maganaɗisu haka yatsan ke janta har zuwa gaban fanfon .

 

Tamkar kayan wanki haka akai jifa da ita gun , amma kuma sai ta samu bokiti cike da ruwa ga tsintsiya gefensa .

 

Cike da tsoro ta sunkuci bokitin ta nufi sashen banɗakunan zuciyarta kamar ta fice dan azabar tsoro .

 

Kewayen nasu guda huɗu ne manne da juna kai tsaye ta nufi na farko , amma sai taji an yi gyaran murya cikinsa , hakan yasa ta san da mutum a cikin toilet din kenan .

 

Sai ta matsa na gabanshi nufinta idan wadda ke ciki nafarko ta fito itama ta gama da wannan sai ta koma ta wanke shi.

Sai dai shima tana matsawa taji ana tari sosai cikinsa , murmushi tayi dan ta fahimci akwai mutane gun tsoronta sai yaɗan ragu ,cikin nishaɗi ta nufi na ukkun shi kuma sai taji alamar zubar ruwa cikinsa tamkar ana wanka .

Fiddo ido waje tayi tsabar mamaki , tasha jin Shema'u na gaya mata wasu na wanka in suka zo makaranta ,taita mamaki ƙarshema ta musa maganar dan a tunaninta ba abu bane mai yiyuwa wanka cikin makaranta ,yau dai ta yarda tun da tagani da idanunta .

ɗan jim tayi ko cikin sauran na farkon ko na biyun wata zata fito tunda an ɗan jima da zuwanta kuma duk ciki ta iske su .

 

Ganin ba wadda ta fito ta taɓe bakinta ta sunkuci bokitin ruwanta ta nufi toilet ɗin ƙarshe .

 

Aje bokitin tayi da zummar buɗe marfin kofar ta shige , tana kamawa taji wani kalan nishi mai ban tsoro na tashi daga cikin toilet ɗin .

Arazane ta saki ƙofar sai dai ta makara ƙofar wangale bakinta tayi da kanta , cikin razana ta kalli cikin toilet ɗin dan ganin mike nishi  cikinsa haka ?

Wata yarinya tagani shekarunta ba zasu wuce nata ba fuskarta baƙiƙƙirin idanunta dara_dara masu ban tsoro hancinta wani dogo mai tsawo naban mamaki ga girar idonta da gashin idanunta sun haɗe sai nishi take tana kwance shame_shame ta miƙo hannu alamar Bilkisu ta isa gareta .

Shi kanshi hannun baiwar Allah baida kyan gani dan wasu zaƙo_zaƙon ƙunbuna ne waɗanda kowane da kalansu , ita dai tasan kowane mutum yatsansa biyar amma yau taga mai yatsu bakwai , girgiza kai tayi da niyar fita daga toilet ɗin amma sai yarinyar ta ƙara kaimin nishinta hannunta tamkar wanda aka ƙarama tsawo ta ƙara miƙoma Bilkisu da wata bahaguwar murya tace "Ki taimake Ni Bilkisu karki barni ,,tana magana fuskarta na sauyawa zuwa ja baƙi .

Haka nan taji ta tsinke da lamarin yarinyar ga zuciyarta dake tsinke .

 

Bata san ya akai ba ta dai ganta ta isa gaban yarinyar ta miƙa ma ta hannu alamar zata tadata .

 

Wani irin shokin taji da hannunta ya taɓa hannun yarinyar abin da yasata furta "A'uzubillahi minasshaiɗanirrajim,, wata ƙara yarinyar tayi ta fincike hannunta daga gun Bilkisun idanunta suka juye zuwa kalai ɗorowa ta buɗe baki da ƙyal tace "bar nan Bilkisu ,, bakinta na fidda hayaƙi tamkar wuta ke ci a cikin bakin nata .

 

Ai bata jira komiba tai baya da gudun tsiya , bata tsaya ko ina ba sai bakin kofar fita gun gaba ɗaya .

 

Daidai nan duka ƙofofin suka buɗe kansu na ciki suka fito waje .

 

Wani sanyi taji a ranta ko banza ta samu waɗanda zasu taimaka mata ko basu tayata ba zasu jirata ta gama aikinta sannan kuma waccen Yarinyar bazata cigaba da bata tsoro ba .

Gama wannan tunanin kenan ta buɗe idonta cike da ƙwarin gwiwa ta sauke su kan kofar toilet din uku baki ɗaya kasancewarsu a jere suke .

 

Zumbur ! Ta miƙe tana nunasu da yatsa fuska cike da mamaki tare da al'ajabi , ba komi ya bata mamaki ba illa ganin yarinyar ita ce ta fito daga kowane banɗaki cikin wani mummunan yanayi hawayen jini na fitowa daga fuskarta , tana miƙo hannu alamar Bilkisu ta isa gareta .

 

Tasha ganin yaran da Aljanu suka shiga a cikin makarantar tasu kowace rana sai an kirata taima wata karatun Alkur'ani , yau gashi ta ga zahirin gaskiyar maganar Shema'u dake cewa "duk rintsi ban shiga banɗakin makarantar nan gara na matse ko miye naje gida hankali kwance nayi komiye da dai in shiga Aljanu su samu ta ƙari,,

 

Lokacin taci dariyar maganar Shema'u dan har tambayarta tayi "Anfaɗa maki  toilet ɗin gidanku babu Aljanu kenan ?

Itama Shema'u cikin dariyar tace "Ai garasu mun saba sun san nan gidanmu ne dan haka basu yi mana komi ,,

 

Ji tayi an taɓota ta bayanta , bakinta cike da sunan Allah ta juya .

Ya Salam ! Itace kalmar da ta furta ganin wata yamutsatstsiyar tsohuwa bayanta da ido ɗaya tana kallonta ,

 

Runtse idonta tayi tafara karanto suratul junnu (kulhuyiya)da karfi .

Bata saurara da karatun ba sai da taji an kaɗa karaurawa ta fita breakfast ,

 

Ahankali ta buɗe idon ba kowa ba alamar komi sai ita kaɗai hatta bokitin ruwan babu shi gun kwata_kwata , ai bata sake saurarawaba ta kwasa da gudu tai waje ta bar harabar gun jikinta na rawa .

 

Daga can nesa Shema'u ta hangota ta kwaɗa mata kira ,cikin sauri ta nufi gunta bakinta ɗauke da labarin abin da ya faru .

Amma tana zuwa ta ji ta kasa bayyana ma ta gaskiyar lamarin saima shaidata mata yanda ta wanke toilet din da kyau da tayi .

Cikin dariya Shema'u tace ai "Sir Muntasir ta kanki ya fara aiki daga zuwansa kinga saimu kiyayi kanmu musanman ni da bansan harƙallai da zata saka a sadani da wankin toilet wallahi,,

Yaƙe kawai tayi tana maimaita sunan a zuciyarta Muntasir.

 

Haka dai suka gama break ɗinsu aka kaɗa karaurawa suka nufi class.

 

Cikin tsautsai wani ɗan icce ya riƙe haɓar wandon Bilkisu ga anata gudu malamai zasu shiga class duk wanda malam ya riga shiga  ruwa yake .

Ganin Sir Muntasir ya nufi class ɗinsu yasa Shema'u rugawa tana "Nidai na tafi ga Sir Muntasir can class ɗinmu ,,

 

Bilkisu sai ƙoƙarin cire wandonta take amma yanda kasan mutum ne ya riƙe mata shi ta kasa abin da yasa ta fasa kuka kenan.

 

"Masha Allah,,

 

Itace kalmar da taji anfurta a cikin kunnenta kenan , hakan yasata ɗagowa dan ganin ko waye , amma ba kowa gun .

 

Tana ƙara kallon gun da iccen ya riƙe mata wando taga ba iccen , zaro idanuwa waje tayi da gaske ba iccen ba alamarsa kwata_kwata .

 

Cikin sanyin jiki ta nufi class ɗin su zuciyarta cike da tunani kala_kala .

 

Tana shiga ta iske Sir Muntasir nata darasi , cike da tsoronsa ta nufi kujeraita da nufin zama .

 

"Bilkisu daga ina kike ?

 

Ba ƙaramin kaɗawa hantar cikinta tayi ba jin ya ambaci sunanta , yaushe yasan sunanta ?

 

"Randa na fara ganinki na san sunanki Bilkisu ,,

 

Wayyo Allah! A zuciya tai maganarta amma wai yajita mutum kamar mai kunnen maciji ?

 

"Zaki fito koko sai kinsan kunnen nawa da gaske na macijin ne koko ?

 

Tashin hankali wai mike damuwata ne ni Bilkisu ?

 

Wannan karan tsawa ya daka mata "taya ina maki magana kina can kina maganar zuci ?

 

"Daga yau idan kika ƙara bari na kamaki da laifin makara zaki gane kurenki shashasha fice mun daga class ,,

 

Ba itaba hatta sauran ƴan class ɗin sai da hantarsu ta kaɗa jin amsa kuwai muryaisa .

 

Sum_sum ta fice idanunta na zubar hawayen takaicin malamin , itafa tun da ta ganshi taji bai kwanta ma ta ba sam bata son ganinsa ko alama bai yi kama da  mutumin kirki ba .

 

"Bakiyi ƙarya ba sai dai baki faɗa daidai ba Bilkisu,,

 

Arazane ta dubi kofar class ɗinsu ba kowa ga alama yana ciki amma taya yake jin abin da take faɗi akansa harya bata amsa ?

 

Haka dai Bilkisu ta ƙare ranai da shiga case kala daban_daban duk kuma na Sir Muntasir ne .

 

 

 

Cikin sallama ta shiga gidan nasu fuskarta ɗauke da murmushi , Innarsu dake kason abinci ta kalleta ta watsar kasancewarta ɗiyar fari gunta .

 

Bata tsaya yin komiba ta faɗa tayi wanka ta fito ta dauki abincinta ta koma ɗakinsu , ta kula yau Innarsu bata cikin yanayi mai daɗi sai haɗe mata fuska takeyi tamkar tayi mata laifi mai girma, Allah dai ya maido Babansu ko taji saukin Innarsu .

 

Tun da Bilkisu ta shigo gidan ba da jimawaba wata baƙar guguwa ta turniƙe tsakar gidan Inna na cikin kason abinci taji tamkar ana faɗa dan haka ta ɗago kanta da sauri dan tabbatar da abin da kunnenta ke jiyo ma ta.

 

Wasu kalan yara ta gani su biyu masu falka-falkan kunnuwa da ɗuma_ɗuman kumatu suna rigima kan lallai kowa shine zai fara ɗaukar nashi kason .

Ihu ta kwaɗa ta ruga ɗakinta jikinta ko ina rawa yake .

 

Tana shiga ɗakin ta iske su sai cin abincin suke suna hira tamkar ba sune ta baro waje ba .

Karkarwa jikinta ya kamayi kafin ta yanke jiki ta faɗi gun a sume .

Faduwarta tai daidai da curewar yaran guri guda suka zama wata halitta guda mai ban tsoro ta fashe da dariya ta zama hayaƙi ta shige jikin Innar.

 

 

 

Tofa Inna ke da matsala ko Bilkisu ?

 

 *Taku dai ce Haupha*