MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 56--60

Hakan yasa ta fusata iyakar fusata ta koma kai tsaye dajin da su Bilkisu suke zaune ta shiga da nufin nuna ma Jalal ta yi nadamar abin da ta aikata gare shi da Bilkisun don ta samu Bilkisun ta maida mata Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash suffarta sai ta dawo ta sace Bilkisun ta kaima Sarki Zayyanul murrash ɗin ya kashe ta kamar yadda suka tsara.

MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 56--60

Page 56----60

 

Cikin lokacin komi ya sauya ga rayuwar Bilkisu da Abduljalal bin Uwais, ko da yaushe cikin kuka da damuwa take akan samun haihuwa amma shiru babu wani labari.

 

Hatta soyayyar da suke ma juna ta ja baya don ko da yaushe baƙin ciki ne kwance akan fuskarta, ita dai burinta ta samu haihuwa.

 

Abduljalal bin Uwais ya rame ya ƙanjame ya fita hayyacin shi akan damuwar da Bilkisu take ciki ya rasa yadda zai yi da damuwar nan ta Bilkisu, domin shi mutum mai cika alƙawarin da duk ya ɗauka, ga shi yana neman kasa cika alƙawarin daya ɗauka akan dauwamar da ita ce matsalarta a yanzu shi kuma alƙawarin dauwamar da farin ciki yayi a tsawon rayuwarta.

 

Ko da yaushe yana tuna maganar malamain akan babu haihuwa tsakanin mutum da aljani, kenan yanzu ya zai yi da alƙawarin daya ɗaukar mata ? Tabbas idan ya barta a haka bai cika alƙawarin ba, amma kuma ya zai ya cika shi ? Idan har yace zai cika alƙawarin nan to tabbas hakan na nufin rabuwarsu ce ta zo.

Shi kam yana jin da ace ya rasa Bilkisu gara ya rasa farin cikin shi sai yafi murna da son hakan.

 

Ko da yaushe tunaninsa kenan ya kasa samun mafita kuma kan lamarin domin kullum Bilkisu ƙara shiga damuwa take .

 

 

 

 

   Darul Islam

 

 

Yau Nasir tunda gari ya waye yake kwance tunanin gida da masoyiyarsa Bilkisu kawai yake.

Ya ƙi cin abinci ya ƙi kula kowa ciki hadda abokin na shi Yuzarsef shima ya rasa gane damuwar abokin nasa yau, don haka shima sai ya samu kansa cikin damuwa har ya fara tunanin hanyar da zai fitar da Nasir ɗin daga cikin dajin.

 

Sai dai yasan hakan tamkar ganganci ne da rayuwarsa zai yi, domin ba abu mai sauƙi bane fita daga cikin dajin salin alin.

 

Amma kuma yau ganin Nasir ya damu iyakar damuwa sai ya ji ƙwarin gwiwar fitar da shi daga dajin ko da kuwa zai rasa ransa ko ya fuskanci hukunci mai tsauri .

 

Hakan yasa ya ja hannun Nasir ɗin suka kauce sauran aljanun dake gun zuwa inda ba kowa ya fara tambayar Nasir ɗin .

 

"Shin idan na fitar da kai daga na kana da ƙwarin gwiwar da zaka iya tunkarar duk abin da zai biyo baya ?

Shin zaka iya jure yaƙi da aljanu ?

Shin zaka iya gudun ceton ranka babu ci babu sha na wasu kwanaki ?

 

Idanu ya zubama Yuzarsef ɗin yana jin ya shirya zai iya komi indai akan barin shi dajin nan ne.

 

Yuzarsef ɗin ya duba yace, "Tabbas zan iya komi amma fa ka sani ba zan koma gida ba sai da Bilkisu, don haka duk inda ya ɓoye ta sai na je na ganota sannan zan koma gida tare da ita ."

 

Kallon baka da hankali Yuzarsef ke binshi da shi.

 

"Nasir kana nufin zaka iya ja da Yah Malam Kenan ?

Ka kuwa san waye shi ?

To bari na tuna maka shi ne Sarkin fararen Aljanu dake wannan nahiyar baki ɗaya, sannan a ƙarƙashin mulkinsa yana da manyan birane masu shaƙe da manyan mayaƙan Aljanu masu fushi da fushin wani.

 

Sarki Abduljalal bin Uwais shi ne matashin Sarkin da tunda yake ba a taɓa cin shi da ya ƙi ba, sai shigowar rayuwar Bilkisu a rayuwarshi .

 

Don haka ka  cire maganar tunkarar shi da sunan yaƙi don babu abin da zaka samu daga gare shi sai faɗuwa."

 

Ko alamar jin kashedin bai nuna ba.

Don haka ya miƙe tsaye rai ɓace yace cike da jarumta.

 

"Na rantse da Allah akan Bilkisu ni nan sai na sauya tarihin Sarkin naku ta hanyar shayar da shi ruwan mamaki na gaske !

 

Ni fa akan Bilkisu na shirya barin duniyar baki ɗaya, ka kuwa san wace ce Bilkisu a wajena kuwa ?

 

Yuzarsef sai ya samu kanshi da mamakin jarumtar Nasir ɗin yadda da gaske yake akan batun Bilkisun nan.

 

Ganin Nasir ɗin na neman tara ma shi sauran abokan nasu yasa ya bar shi gun ya wuce yana tunanin hanyar da zai tsiratar da abokin na shi .

 

Nasir kuwa ya kasa zama sai kaiwa da komowa yake har aka aiko kiran shi in ji malaminsu.

 

 

Aljana Suwaibatul Zabbar kuwa ta yi duk abin da ya kamata tayi amma ta kasa maida Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash ainihin suffarta .

Hakan yasa ta fusata iyakar fusata ta koma kai tsaye dajin da su Bilkisu suke zaune ta shiga da nufin nuna ma Jalal ta yi nadamar abin da ta aikata gare shi da Bilkisun don ta samu Bilkisun ta maida mata Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash suffarta sai ta dawo ta sace Bilkisun ta kaima Sarki Zayyanul murrash ɗin ya kashe ta kamar yadda suka tsara.

 

Sai dai tun daga kan fadawan masarautar ta fahimci akwai damuwa tare da Jalal ɗin duba ga yadda hadimansa suke sukuku ba walwala wanda duk sanda aka ga hakan to shima bai da natsuwa balle walwala.

Sai jikinta yayi sanyi ta samu kanta da jin faɗuwar gaba, kada dai ace bai da lafiya Jalal ɗin fa.

 

Haka taita ratsa fadawan tana wucewa harta isa inda take tunanin iske Jalal ɗin, duk da tayi takaicin iske shi da Bilkisu amma haka ta daure ta isa gabanshi ta durƙusa tana ba shi haƙuri akan abin da ta aikata gare shi.

Kasancewar daman yasan dole hakan zata faru duba ga yadda take matuƙar ƙaunarsa yasa ya amince da tubanta yace ba komi ya wuce.

 

Bilkisu ta kalla itama ta nemi yafiyarta duk da tana mamakin abin da ya fitar da su daga hayyacinsu su duka sukai rama lokaci guda.

 

Itama Bilkisu ganin Abduljalal ɗin ya yafe mata itama sai ta yafe mata ta maida kanta cikin jikinshi ta kwanta tana jin zuciyarta na mata ciwo kan damuwar da kullum take ciki.

 

Ko yanzu haka kuka ta gama tana ba shi labarin mafarkin da tayi na ta haihu yara biyu mace da namiji shi ne abin yasa ta kuka sosai tana tambayarsa yaushe ne mafarkinta zai tabbata ne ?

 

Ya rasa yadda zai ita sai haƙuri yake bata sai ga Suwaibatul Zabbar ita ce tasa ta daina fitinar kukan ta natsu yanzu.

 

A hankali ya kwantar da ita ya fice daga ɗakin yana jin ya  kamata dai ya haƙura da farin cikinsa domin ɗorewar na masoyiyarsa.

Wani ɗaki ya shige ya dinga kuka yana buga kanshi ƙarshe yayi ma kanshi jina-jina kana ya fice bai zame ko ina ba sai Darul Islam kai tsaye ya gaya ma Malamin a sallami Nasir a sa wasu su kai shi gidansu, sannan a gayama aljanin dake aiwatar da aikin Nasir ya dawo .

 

Ya fice yana matuƙar jin ƙunci da mugun baƙin cikin abin da yake nufin aiwatarwa gare shi da masoyiyarshi.

 

Gunta ya koma tana ta sharar barcinta tana ajiyar zuciya ya kalleta da kyau ya sake hawaye suka zubo ma shi ya shige cikin jikinta yana jin tamkar yayi mazansa a hakan ba tare da ya bayyana ba har ƙarshen rayuwar shi, amma hakan ba zai samu ba domin kuwa shi ne Sarki ba yadda za ai yayi hakan .

 

Haka yayita shawara yana sakewa har ya gaji yaFito daga jikinta ya tasa ta gaba yana kallo ƙarshe ya fara hura mata iska .

A hankali ta fara motsawa daga ƙarshe ta buɗe idanunta ta sauke su a kansa.

 

A hankali ta tashi zaune tana kallonsa , kawai sai gabanta ya dinga faɗuwa akai-akai.

 

Cikin natsuwa ya dubeta, bayan ya ɗauko duk wata jarumta da juriya ya aza ma kanshi.

 

"Bilkisu a yau dai na samo maki mafitar damuwarki, ko ince damuwarmu.

Kamar yadda kika sani nayi alƙawarin kulawa dake tare da saki cikin farin ciki tsawon rayuwata da taki rayuwar, to a yau zan tabbatar da hakan gareki .

 

Bilkisu kina son ganin jininki na yawo a doron duniya sai dai ki sani idan ina tare da ke ba za ki taɓa samun haihuwa ba kamar yadda aka gayamin.

 

Don haka na yanke shawarar haƙura da nawa farin cikin na zaɓi naki farin cikin ta hanyar yanke duk wata alaƙa ta dake na maida ki duniyarku, ki je ki auri masoyinki ki samu cikar burinki wato ƴaƴan cikinki Bilkisu.

 

Hawaye suka zubo ma shi bai damu da gogewa ba ya cigaba da cewa.

"Zan maida ki gidanku haka zan maida ki ga masoyinki Nasir domin kuwa yana wajena tun lokaci mai tsawo.

 

Ina son ki yafe min duk abin da nayi maki a tsawon zamanmu dake Bilkisu.

 

Tunda ya fara magana Bilkisu ke girgiza kanta tana wani irin kuka mai tsuma zuciya.

Ni kam indai haka na ta yafe haihuwar baki ɗaya, zan zauna babu haihuwar indai sai na rabu da kai ne zan haihu Abduljalal domin ina sonka so na gaskiya bana wasa ba.

Ka sani indai aka wayi gari babu kai kusa dani to tabbas na shiga cikin taskun rayuwa da tashin hankali mai ɗorewa.

 

Abduljalal kasan cewar kaine fitila mai haskamin rayuwata, kai ne wanda nake gani farin ciki ya bayyana gareni to ya kake tunanin zan yi idan baka a kusa da ni ?

 

Ka sani cewa a yanzu babu wani masoyina wanda nake so sama da kai, asalima ni yanzu zuciyata ta manta kowa a fagen soyayya inba kai ba.

 

Don Allah kada ka rabamu Abduljalal don Allah !

 

Da gudu ta ruga ta shike jikinshi tana wani irin kuka mai ratsa zuciya.

Rungumeta yayi sosai shima ya saki kukan mai tsuma zuciya.

 

Suwaibatul Zabbar tana laɓe tana jinsu itama sai ta samu kanta da tausaya masu baki ɗaya, bata ankara ba ta ji hawayen tausayinsu na zubowa daga idanunta.

 

 

Sun jima suna kuka suna masu ƙanƙame junansu abin gwanin ban tausayi, a hankali ya hura mata wata iska  nan take barci mai nauyi kama Bilkisun.

 

Cikin sanyin jiki ya kira wasu aljanun mata ya ba su umarnin su kaita gidansu cikin ƙoshin lafiya.

 

Suna fita da ita ya ɗaga murya yace, "Sai wata rana masoyiyata zan yi kewarki sosai !

 

Kuka yake yana buga kanshi da ƙarfin gaske a bangon ɗakin nan da nan Suwaibatul Zabbar ta shigo ɗakin ta kama shi ta rungume shi tana lallashinshi kamar ƙaramin yaro.

 

 

Kamar daga sama wata iska ta dinga kaɗawa nan take sai ga jikin Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash yana ɓambarewa, sai da ya gama ɓambarewa sannan sai ga jikinta ya bayyana yadda yake na asali.

 

Tana ganin ta koma yadda take ta zama iska kai tsaye ta kama hanyar dajin mahaifinta cikin sauri.

 

 

    Nasir

 

Nasir na zaune gaban malamin dake koyar da shi karatu, ya dube shi yace, "saƙo ya zo mana na cewar a yau ko ince a yanzu mu maidaka cikin jama'arka cikin aminci da kamala don haka ka zaɓi wanda kake son ya maidaka gida a cikin jerin matasan aljanun da kuke karatu tare.

Wani farin ciki ya bayyana a fuskarshi marar misaltuwa cikin ɗoki yace Yuzarsef ne ya zaɓa ya maida shi gida.

 

Aikuwa haka akayi nan take yayi bankwana da sauran ɗaliban ya haye bayan Yuzarsef suka ɓace a sararin samaniya.

 

 

 

Gidansu Bilkisu

 

Inna Huraira na zaune ta ji wani ƙamshi irin na turaren miski ya gauraye gidan baki ɗaya.

Nan da nan ta fara karanto addu'ar neman tsari daga sharrin shaiɗanun Aljanu da abin ƙi.

 

Kamar an ce ta shiga ɗakinta sai ga Bilkisu kwance cikin kayan sarauta sai barci take, tayi haske tayi matuƙar kyau duk da ba sosai take ganinta ba.

 

Cikin farin ciki ta dinga furta, "Alhamdulillah ! Masha Allah !

 

Sai da ta leƙa ta tabbatar da Bilkisun ce sannan ta fice zuwa ɗakin Malam dake ta karatun Alkur'ani .

 

Cikin sallama ta shiga tayi ma shi albishir da ganin Bilkisu cikin ɗakinta.

 

Jin abin da ta ce yasa Malam kabbara sallah raka'a biyu ta godiya ga Allah .

Sannan ya fice cikin hanzari zuwa ɗakin Hurairar.

 

Tana kwance sai barci take hankali kwance tasha kayan sarauta a jikinta sai ƙamshin turaren miski take, ashe shi ne ya buɗe gidan da ƙamshi.

 

A hankali ya dinga kiran sunanta, "Bilkisu ƴar albarka.

Can cikin barci taji ana kiran sunanta a hankali ta buɗe idanunta ta sauke su a kan iyayenta.

 

Zumbur ta miƙe tsaye tana ƙarema ɗakin kallo, kuka mai karfi ta fashe da shi tana kiran sunan Abduljalal cikin ɗaga murya.

"Don Allah kada kai min haka na amince zan cigaba da rayuwa da kai a hakan Abduljalal."

 

Babanta ya kamota ya rungumeta yana tofa mata addu'a a saman kanta.

 

Ita dai sai kuka take tana kiran sunan Abduljalal ɗin ya zo ya tai da ita.

 

Sai jikinsu yayi sanyi kenan ita bata so suka dawo da ita ba kenan ?

 

Malam yayi ta lallashinta yayin da Huraira ta fice don zuwa gidansu Shema'u da gidansu Nasir ta gaya masu cewar Bilkisu ta dawo.

 

Shema'u kamar ta zuba ruwa ƙasa tasha don murna da Inna Huraira ta gaya mata ƙawarta Bilkisu ta dawo.

 

Daga nan sai gidansu Nasir inda suka iske gidan cike da mutane ana ta murna Nasir ya dawo, ya zama tamkar wani Balarabe don kyau da haske da yayi sai kace ba shi bane ba.

 

Ai yana jin Bilkisu ta dawo sai ya miƙe yace ya tafi sai sun taho .

 

Yana zuwa gidan ya iske mutane sun cika gidan amma kowa jikinshi yayi sanyi saboda kukan da Bilkisu ke yi na ita sai ta koma gun masoyinta Abduljalal.

 

Kawai ganinshi akai ya zauna yana maida numfashi .

 

Me yasa Bilkisu zatai ma shi haka ?

Kenan ta daina son shi ?

 

Da ƙyar ya samu ya saita kanshi ya isa gareta yana mai ɓoye duk wani ɓacin ran dake damunsa na kukan da take da abin da take cewa.

 

"Ibnah gani gareki ki daina kuka don Allah kin ji ?

 

Kallon shi take tana san tuno waye gareta ma ?

 

Nasir !

Cab wallahi na tsaneka ban sonka a yanzu na fi son Abduljalal da kai !

 

Huraira ta sauke mata mari mai kyau a fuska ta ce cikin faɗa, " Ba ki da miji sai Nasir indai muna raye."

 

 

To ko ya zata kaya ?

 

Haupha