MAMAYA; Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani Fita Ta 48--50
Page 48___50
Malam Ahmad ganinsu Huraira hajaran majaran yasa gabanshi faɗuwar bazata, ko shakka babu Bilkisu na cikin gararin rayuwa a yadda yake ji a jikinsa.
Huraira ta isa da ƙyar ta zauna kusa da Malam ɗin tana kuka tana ce wa, "Malam ka ji ko ? Ka ji yaron can shima gidansu ba a san inda yake ba ko ? Haƙiƙa duk inda yake yana tare da yarinyarmu, ba zan taɓa yafe masa ba."
Sai kan Malam Ahmad ɗin ya sake ƙullewa sosai da sosai, to me hakan ke nufi ne ? Tare suka ɓace koko da abin da ya same su a lokacin da suke tare ? Shi kam bai jin wani alamar rashin gaskiya a tare da yaron a ransa, sai dai yana jin cewar akwai mummunan lamarin da ya afku a garesu .
Don haka ya dubi Huraira da Shema'u dake kuka yace, "Ku daina kuka ku cigaba da yi masu addu'a, domin haƙiƙa ina jin cewar suna cikin mugun yanayi a jikina.
Inna Huraira ta share hawayenta ta ce, "Malam kai daman ka yarda da yaron don haka Allah ya jisshe mu alheri to, ni kam duk na karaya da lamarinsa tuni wallahi, don ba zan manta randa ya zare bindiga ba ya nuna ni da ita tsirararta yace mun, "Ni da kike gani aikina ya ban damar kashe duk wanda naga dama, kuma abin da baki sani ba shi ne idan na kashe ma kuɗi ake ban masu dama, don daɗin kashewar da nake ake ji, don haka ɗauke kan nan naki da ba komi cikinsa sai zallar masifa ba abin da zai ƙaramin sai rank." Ta yamutse fuska ta cigaba da cewa, "Ni ban san ko miye Rank ɗin ba, da yake nufi don haka nake matuƙar shakkar yaron ni."
Duk da suna a halin jimami sai da Malam ya murmusa , mai hali dai bai fasa halinsa sai dai yayi sauƙi.
Shema'u ta ce, "Inna shima fa wai ya bar komi nasa a cikin ɗakinsa, ko wayarsa ta hannu bai ɗauka ba, don sun ce cikin dare ya fice daga gidan ma don da shi aka kwanta."
Ƙarshe dai suka ɗauki buta su kai alwalla malam ya ja su sallah Shema'u ta wuce gida tana cike da alhinin lamarin ƙawar tata.
Ba wani ɓata lokaci akai ta yaɗa jita-jitar Bilkisu da Nasir sun gudu saboda yayi mata cikin shege .
Lamarin da ya saka iyayen Nasir a mawuyacin hali kenan domin suna da tabbacin yaronsu na da natsuwa haka bai da kule-kulen mata kamar yadda ake ma sauran ma'aikatan su shaidar kula mata barkatai, ƙarshe dai iyayensa suka haɗu da na Bilkisu domin tattauna lamarin yadda ya kamata.
Anan ne Malam Ahmad ya rantse ya maya kan cewar bai yarda da Nasir guduwa yayi da Bilkisu ba, amma ya yarda da cewar akwai abin da ya faru dasu marar daɗi.
Nan suka yanke shawarar sakawa ayi masu addu'a a masallatai da makarantun islamiyya don bayyanar yaran nasu.
Duk abin da suka tattauna akan idon hadimar aljani Abduljalal bin Uwais wato Bariratul azam tayi murmushi ta ɓace bat tana jinjina yadda mahaifin Bilkisu ke da kaifin basira da tunani.
Nasir.....
Yana cikin kutsawa cikin dabbobin yana wucewa ya ji wata irin magana wadda bai san irinta ba, haka bai san abin da ake cewa ba, don haka sai ya juya don ganin mai maganar .
Wasu mutane ya gani su uku amma kamar ba mutane ba, domin yadda suke da kyau ga wani irin idanuwa da hanci sai dai basu da yatsun ƙafafuwa, ko alama ƙafarsu a shafe take .
Kallonsu yake yana aiyana yadda za su kwashe da su idan da faɗa suka zo gare shi domin dai yanzu ya amince ba mutane ba ne duba ga yadda yaga kamar suna sauya kama lokaci zuwa lokaci a cikin idanuwansa.
Ganin bai fahimtar abin da suke cewa yasa ya juya ya cigaba da tafiya abinsa .
Sai dai ko taku biyar bai ba ya sake cin karo da su a gabansa, sai dai wannan karon su biyar ya gani cikin fararen kaya masu ado da ƙyalƙyali.
Yanzu kuma sai ya ji kamar larabci suke masa kasancewar yana jin kaɗan-kaɗan larabcin.
Don haka ya fahimci tambayarsa suke ina za shi a cikin wannan dajin ?
Shima a cikin gwarancin larabcin nasa ya bayyana masu zai fice ne zuwa bakin hanya ko ya dace da hanyar da zata kai shi gida.
Kallon juna sukai su kayi dariya suka ce, "Ai ba inda zaka bi ka fita daga cikin wannan dajin, domin kana cikin dajin Darul Islam wanda matasan Aljanu ke karatu acikinsa, duk aljanin da aka kawo wannan dajin sai yayi shekaru arba'in da biyar sannan zai iya fita daga cikin wannan dajin.
Kasancewar ba komi yake iya ganewa a larabcin nasu ba yasa ya kasa fahimtar bayanin nasu yadda ya kamata, hakan yasa ya gaya masu bai fahimci abin da suke nufi ba sam.
Nan dai su kai ta gwarancin da zai iya fahimta har ya fahimtar .
Dafe kansa yayi yana jin matuƙar ciwo a zuciyarsa, tabbas akwai luguden masifa tsakaninsa da Abduljalal bin Uwais ɗin, domin ba aljani ba ko wuta ne shi bai isa ya raba shi da Ibnah a cikin duniyar nan ba, yana fatar ko bayan sun mutu ta zama uwargidansa a gidan aljanna .
Wani daga cikinsu ya kama hannunsa ya nufi wata hanya da shi, ba su jima suna tafiya ba, sai ga su sun ɓulla cikin taron aljanu kada daban-daban, kowa da abin da yake.
Nan da nan kallo ya koma kansu, shi dai biye yake da wanda ya kama masa hannu kawai suna tafiya ba tare da sun ma juna magana ba.
Wani gida suka nufa mai kyau wanda shi bai taɓa tunanin akwai sa a cikin irin wajen ba sam.
Suna shiga cikin gidan mamakinsa ya ninku fiye da na ganin gidan, domin kamar wata babbar masarauta haka cikin gidan yake, ga wasu kyawawan mutane zaune sai karatu suke mai matuƙar daɗi da daɗin saurare cikin tattausar murya mai cike da natsuwa.
Gaban wani tsoho suka isa wan can ya kai gaisuwa sannan yayi masa jawabin da bai fahimci komi a maganar ba, domin da irin yaren da suka fara masa magana ne yayi masa magana,shi ma da shi ya maida masa.
Bayan sun kammala ne mutumin ya dubi Nasir da larabcin yace, "Anan zaka cigaba da zama domin an kawoka ne domin ka cigaba da karatu kaima ka zama ɗalibi a cikin wannan makaranta da Darul Islam."
Sai ga tarin littattafai na addini jibgi guda an aje kusa da shi, an tabbatar masa da duk sai ya gama karanta su akwai wasu ma idan ya gama da su ɗin.
Baki ɗaya sai hankalinsa ya tashi ainun, akan me za a ce zaman karatu aka kawo shi yayi ?
Ina iyayensa ina aikinsa ? Ina maganar masoyiyarsa ? Wannan ai tsabar rainin hankali ne irin na aljanu, to haƙiƙa akwai yiyuwar ɓallewar rikici mai tafe da masifa a cikin makarantar ta su.
Wani saurayi ne ya zo ya bashi hannu su gaisa, bai hana ba ya miƙa nashi hannun, suka gaisa.
Saurayin yayi murmushi yace, "Sunana Yuzarsif na ganka a cikin wannan makaranta na ji ka birgeni idan ba damuwa ko zamu iya zama abokai ? Ban da shekaru masu yawa ni yaro ne duka-duka shekaruna ɗari takwas da tamanin da bakwai, kai fa ?
Tashin basasa kenan.
To shi duka-duka ashirin da bakwai garesa amma mai ɗaruruwa na ambatar kansa yaro ina ga shi ? Don haka ya haɗiye miyau da ƙyar yace, "Indai hakane to ni ban ko leƙo duniyarba gaskiya yanzu ake tunanin haifar zuriyar kakana na ɗari da bakwai kafin a zo kaina."
Dariya aljanin yayi cikin natsuwa yace, "kasan ban gane komi a cikin maganarka yanzu don larabcinka bai yi sosai ba, amma insha Allah zan koya maka indai muna tare."
Nasir ya dubesa tsakiyar ido yace, "idan na gudu fa bama tare ?
Saukar mari ya ji a kumatunsa, an bashi amsa da Hausa kamar yadda yayi furucin da Hausa.
"Babu inda zaka je domin Sarki ya bamu ajiyar ka yace a kula da kai ban da cutarwa gareka haka yana son ka zama masanin addini ta kowane fanni don haka ka kiyaye ambatar kalmar fita daga cikin Darul Islam."
"To ya maganar aikina fa ? Ina maganar iyayena da sauran mutanena ?
Aikinka mun tura madadinka baka da matsala amma maganar iyaye ba abin da ya shafe mu ka ji da kanka kawai."
Daga ranar Nasir ya shiga cikin ɗaliban Darul Islam karatu ba ji ba gani. Cikin ikon Allah sai ga Nasir halshensa ya kare da larabcin sosai ba wanda ya iya Hausa balle turanci a wajen, da Larabci kawai suke magana .
Cikin zafin naman gaske Aljana Suwaibatul Zabbar ta kawo masu wata uwar rida, sai dai zafin naman Abduljalal bin Uwais ya ninka nata, don haka kafin ta ankara ya warce Bilkisun sun koma gefe ta ridi ƙasa.
Hakan ba ƙaramin sake ɓata mata rai yayi ba, don haka ta ja da baya ta fasa uban ihu, ta yi girgiza, sai ga ta ta koma wata gabjejiyar halitta mai matuƙar ban tsoro da hatsari ta durfaro su kai tsaye tana feshin wani ruwa mai wari da turiri da ganinsa idan ya sauka jikin mutum ba abin da zai hana fatar jikin mutum kwarewa.
Ganin hakan yasa Abduljalal sauya tashi halittar zuwa halittar da tafi tata muni ainun ya saka jelarsa ya warci Bilkisun ya jefata cikin wata jakar fata dake rataye a ƙasan wutsiyarsa.
Kai tsaye suka fara azababben yaƙi wanda sai ka rantse da Allah tarin rundunar aljanu ne ke fafatawa a filin daji cikin nufin juna da mugun nufi .
Dajin baki ɗaya amsa amo yake yadda manyan mayaƙa na jinsin aljanu ke baje kolin faɗa a junansu.
Ita dai Bilkisu tana adane cikin wata baƙar jaka sai wutsil-wutsil take, bakinta ɗauke da fatan nasara ga masoyinta Abduljalal .
Suna cikin fafatawar ne Gimbiya Suwaibatul Zabbar ta shammaci Abduljalal bin Uwais ta warce jakar da Bilkisu take cikinta, ɓat ta ɓace daga gun.
Sai dai kuma tana bayyana taga manyan hadiman Abduljalal ɗin tsaye cikin shirin ko ta kwana, bata damu ba domin ta san a fagen fama Jalal ne kawai ke iya ja da ita shima don kawai ƙarfinsu ya kusan zuwa ɗaya, sai ya haɗa mata da dabarun yaƙi na manya yake iya ƙwatar kansa daga gareta.
Bata jira komi ba ta afka masu da yaƙi, sai dai abin mamaki sun yi tsaye sun ƙi maida mata martani ko alama kawunansu a ƙasa irin yadda suke mata a zamanin suna soyayya da Jalal ɗin.
Hakan yasa taji daɗi sosai ta tabbatar da cewa babu su a cikin faɗan nata da Jalal ɗin, don haka ta saki jikinta ta fito da Bilkisu ta riƙe ta a wulaƙance tana dariyar muguntar kisan da zatai mata .
Wuf taji anyi sama da Bilkisun abin da razanar da ita kenan ta kasa ɗaga kanta taga abin da ya ƙwace Bilkisun daga hannunta .
Sai dai jin dariyar Jalal ya tabbatar mata da shi ne ya anshe Bilkisu daga gareta.
Wata uwar ƙara ta saka ta faɗi a gun tana gunza da gurnani, sai a lokacin hadiman Jalal suka dinga tintsirewa da wata irin mahaukaciyar dariya suna zagaye ta.
Ranta idan yayi dubu ya ɓaci a gun, dan haka ta miƙe cikin fusata da nufin tai masu mai kan uwa da wabi, amma ina labarin ya sha bamban domin wani kalar yaƙi suke mata mai matuƙar wahala da ɓadda mutum a filin daga.
Dole ba dan ta so ba ta arce daga dajin baki ɗaya, zuciyarta na tafasa jikinta duk jini tana samu ta fito daga dajin ta yanke jiki ta faɗi tana mai maida numfashin wahala .
Wani ƙaton tsuntsu baƙi ya ɗauke ta yayi sama, lokaci kaɗan ya ɓace bat.
Tafiya mai nisa sukai tsuntsun ya sauka cikin wani daji mai matuƙar ababen ban tsoro al'ajabin gaske.
A hankali ya sauka ya ajeta lokacin ta gama ida fita hayyacinta sosai.
Girgiza yayi sai ga shi ya koma Sarkin baƙaƙen aljanu Zayyanul murrash.
Wani magani ya ɗauko ya shafa mata a kaf jikinta take ta buɗe idanunta, sai dai sun sauya sunyi matuƙar yin ja jini kwance a cikin su ba kyan gani.
Cikin ɓacin rai ta miƙe tsaye bazata ta kai masa wani uban duka .
Tsawa ya daka mata mai firgitarwa, dole ta natsu ta dinga sauke ajiyar zuciya.
"Ni da ke yanzu abin harin mu guda ne don haka na ceto rayuwarki akan sharaɗin da zan maki guda biyu idan kin yarda ."
Shin Suwaibatul Zabbar zata haɗa kai da Zayyanul murrash ?
Wane mataki ne Abduljalal bin Uwais zai ɗauka akan Gimbiya Suwaibatul Zabbar ?
Ku bibiyi Haupha
managarciya