Kallon sa yayi yana so ya shaidasa amma ya kasa gane inda ya taɓa ganin ko da mai irin fuskar tasa, amma gudun kada ace ɗan uwansu Bilkisun ne sai shima ya washe nasa bakin ya miƙa masa nasa hannun suka gaisa.
Kasancewar Major bai da boye abu cikin ransa dan haka ya tambayesa "Ban gane kaba Aboki amma naga kai ka gane ni kai tsaye ?
Murmusawa yayi yace "Ai gun ƙanwata na samu labarin ka."
Ko da naji, sai dai idan ɗan'uwansu ne. (Abin da Major ke rayawa a ransa kenan)
Tare suka shiga cikin gidan suna magana kamar daman can sun san juna.
Bilkisu na zaune tana karatun Alkur'ani mai girma tsakar gida taji sallamar mutane sun shigo cikin gidan nasu.
Cak ta tsaya da karatun Alkur'anin da take yi, ta kuma gaza amsa sallamar da su kayi .
Inna Huraira dake kwance gefen ɗakinta ganin Nasir yasa ta miƙewa zaune, dan sam bata san yaron na shigowa gidan, yau dan samun waje hada su yi mata gayyar soɗi, aikuwa yau zatai maganin sa harda kwashen abokin nasa.
Kallo guda yai mata ya kauda kansa daga gareta ya fahimci yanayinta tsab, shi kuma ba zai jure tai masa halinta ba .
Dan haka kai tsaye sai ya nufi ɗakin Inna Huraira kanshi tsaye yana murmushin da baka iya fassara ko na miye .
Ɗan daburcewa yah Malam yayi domin so yayi kai tsaye su afka cikin ɗakinsu Bilkisu dan akwai ajiyar da yake son yi cikin ɗakin.
Ita kam Bilkisu mamakin inda Yah Malam ya san Yah Nasir ɗin ta kawai ta ke yi .
Inna Huraira ganin Major Nasir kai tsaye ya shige mata ɗaki kamar na gyatumarsa sai abin ya ƙara bata takaici dan haka ta lallaɓa ta miƙe tsaye da ƙyal (kasan cewar har yanzu rauninta bai warke ba) ta faɗa ɗakin har motsa baki ta ke dan azabar masifa .
Ganin haka dole sai Yah Malam ya maze shima ya shiga cikin ɗakin Innar ba dan ransa ya so ba ko kaɗan.
Major Nasir kai tsaye doguwar kujera ya haye ya ɗan kishingiɗa tamkar ɗakin Innarsu.
Tana shigowa ta fiddo idanuwa waje alamar ɓacin rai kwance a fuskarta ta nuna masa ƙofa.
"Maza-maza ka fice mun daga cikin ɗaki marar kunyar ƙarya.
Saboda tsabar wuce waje da ban takaici shine zaka wuto ni sagam-sagam ka faɗa min ɗaki har da gayyar soɗi? ( Ta kalli Yah Malam da ke zaune )
Kamar bai fahimci faɗa ta ke masa ba tare da kora ya tashi zaune yana dariya .
"Kai Innarmu wallahi duk randa kike jin faɗa ban san nazo gidan nan amma gashi yau nayi rashin sa'ar zuwa na iske ki cikin faɗan."
Ai sai Inna Huraira taji kamar ta jashi ta fitar waje dan takaicin maganarsa.
Yah Malam kam sai sunne kai yake alamar sam bai jin daɗin lamarin dake faruwa cikin ɗakin.
Bilkisu ce ɗauke da ruwan sha masu sanyi ta aje masu , ta sunkuya kaɗan ta gaidasu, ta miƙe zata fice Major Nasir ya dube ta cike da walwala yace.
"Ɗiyar Inna kin yi kyau, me Innar tamu ke baki mai daɗi yake saki kyau haka ?
Ita dai murmusawa kawai ta ke yi dan ya bata kunya .
"Yau na shiga uku na lalace ni Huraira gabana kake wannan rashin kunyar ?
Ai sai ta kama dacewa ita ala dole kuka ta ke yi .
Jikin Bilkisu sai ya ɗauki kyarma, har ga Allah bata san ganin Innar tasu a damuwa balle ta ga kukan ta .
Sarai yasan ba kukan gaske ta ke ba, amma ganin gimbiyar tashi ta damu sai ya wayance ya dubi Innar yace...
"Inna miye abin kuka daga zuwana ?
Bari na wuce daman wata mata ce zan halbe shine naga nan cikin unguwar ne dan haka na shigo kafin lokacin halbeta yayin." (Yana magana yana gyara ƙaramar bindigarsa )
Muƙut Inna ta haɗiye wani munafikin miyau da taru lokaci guda a bakinta.
Wuf ta zabura zata bar ɗakin jikinta har rawar disco yake dan azabar ɓari.
Sai dai kuma wajen ta miƙe tsayen idanunta suka hango mata kafar wanda suke tare da Nasir ɗin.
Toshe bakinta tayi da ke niyyar ƙwaɗa ihu, ta sake kallon ƙafarsa tana fatan ace ɗazu gizo idanuwanta sukai mata.
Kafarsa ta gani wata ƙimemiya sai wani uban gashi irin na tumaki kwance a saman kafar tasa, ga wasu kofatai da ta gani madadin yatsu biyar a kafar nashi.
Numfashinta ya kusan ɗauke wa ta kalli mai ƙafar taga idanunsa fari fat babu ko ɗigon baƙi a cikinsu ya kafe ta da su yana ta kallonta ko ƙyabtawa bai yi .
Cikin matukar ladabi Inna ta ce " Sannun ku yaran kirki kune tafe gidan namu ? Lale maraba da ku."
Bilkisu sai taji daɗi dan bata san abin da Innar tasu ke ma Yah Nasir ɗin ko alama yau gashi hada abokinsa kuma Malaminta yake tafe amma taso ta ci masu mutunci.
Ko da yake ta fahimci ganin bindigarsa ce yasa ta koma hayyacinta.
Inna kuwa ban da kukan zuci babu abin da take , ji take tamkar ta kwasa da gudu ta bar gidan.
Wato daman tsinannen yaron nan aljani ne dan haka yake bibiyarta ba dare ba rana ?
To yau dai anyi walƙiya taga komi, dan haka zata miƙe tsaye kan lamarin wallahi ba zata bari aljani ya aurar mata ɗiya ba duk rintsi duk wahala zata bazama iyakar karfinta ta halakar da shegen aljanin nan kafin ya hakalar da ita.
Da ƙyal Inna ta yunƙura ta bar ɗakin tana ta saka masu albarkai dole .
Ai tana fita ta ganta tsakar gida sai ta ari na Zomo ta watsa da gudu ta faɗa maƙwabtansu tana haki da huttai kamar ta ci uban gudu ta gaji har ta gode Allah.
Tambayarta ake abin da ke faruwa sai zare idanuwa ta ke tana nuna hanyar gidanta, lamarin da ya basu tsoro kenan suka kwaso suka nufi gidan nata da zummar ganin abin da ke faruwa.
Malam suka gani zaune yana jan carbi, ya dube su yace "lafiya kuwa kuke ta gudu ?
Inna tai wuri-wuri tana sunne kai ƙasa, dan ta gaza magana ko bayyana abin da ta gani sam.
Malam ya dube ta girgiza kai yace "Allah ya shirya ki Huraira halinki da ban da na sauran mutane."
Ai jin haka sai jikin maƙwabtan yayi sanyi ƙalau suka juya ba ko bankwana suka shige gidansu suna jin nadamar biyo Huraira kai tsaye ba wani bincike .
Suna juyawa suka shige sai Huraira ta bi Malam da ya shige zauren gidan, sai da suka je tsakiyar zauren ya waigo ai Inna Huraira sai ta kwartsa ihu ta zube gun sume .
Ba komi ya sa ta sumewa ba sai ganin fuskar Malam ta koma fuskar ƙaton biri mai ban tsoro ya wangame mata baki kamar zai haɗiyeta, ga wasu halsuna marassa adadi da ke yawo cikin bakin nasa .
Cikin gidan kuwa, hankali kwance sukai ta fira abinsu, sai dai tsakanin Bilkisu da Major Nasir kowa na san tambayar kowa yanda yake da Yah Malam amma tambayar ta tsaya iyakar zuciyarsu ta ƙi fitowa waje.
Gashi dai sai labari suke suna dariya, wasu abubuwan idan Major na faɗi sai Yah Malam ya ida bada labarin abin kamar yana gun akai abin .
Sun jima kana sukai ban kwana ya aje mata tsarabarta suka fice .
Suna zuwa tsakar gidan suka ci karo da Inna ta shigo kamar a tsorace ta shige ɗakin Malam ta turo .
Bilkisu ta koma ɗaki dan bata iya kaisu har kofar gidansu kunya ta ke ji gaskiya .
Suka fice kowa da tunaninsa a cikin zuciyarsa da abin da yake rayawa.
Suna zuwa Kofar gidan sukai ban kwana, Major Nasir ya shige motarsa ya wuce ya bar Yah Malam tsaye kofar gidan tamkar dai rakoshi yayi shi komawa cikin gidan zai yi .
Inna na ɗakin Malam sai kuka ta ke kamar wata ƙaramar yarinya hada su majina.
Malam da dawowar sa daga kasuwa kenan ya shiga ɗakinsa ya ga wannan al'amari na kukan Huraira.
Sai abin ya bashi haushi ya dube ta fuska ba alamar wasa yace " Huraira wa ya bugeki yau kuma ?
Tsabar takaicin tambayar Malam ɗin yasa ta tashi zaune tana kallonsa bakinta ɗauke da tujara tace ...