MAMAYA: Labarin Soyayyar Aljani Da Mutum, Fita Ta 28 Zuwa 30
Page 28____30
Nasir na kwance yana tunanin halin da yabar masoyiyarsa, jiyake kamar ya aje aikin dan yanzu ya fara takura masa gun kusantar Ibnarsa duk sanda yaso ko yaga dama, misali ranar da suka rabu asibiti ya dawo gida ya hana ƙannensa zuwa gidansu yana da burin washe gari ya kwashesu suje baki ɗaya sai ga wayar gaggawa daga office ɗin su ana nemansu da gaggawa,dole ya shirya ba dan yaso ba ya wuce, abin takaicinsa guda ya kira number Ibnar tasa a kashe kada ace dai ciwon dawowa yayi ? Gaba ɗaya ya rasa kuzari da walwala duk a takure yake dan haka yaransa ke baya-baya dashi musamman da suka fahimci yana tare da damuwa,sai kowa ya kama kansa, dan Nasir ba baya gun zuciya da fusata bai cika wasa ba.
"Tunda na haɗu da yarinyar nan komi ya lalace mun, na rasa da dama daga kimata da darajata ni kam nayi alƙawarin shirya mummunan sakayya gareta domin samun sauƙin yanayin data jefa rayuwata cikinta. Gaba ɗaya sun sadda kansu ƙasa suna saurarensa a ƙalla yau anyi wata biyar Sarkin nasu ya kasa aiwatar da abin da yake cewa zai aiwatar, tabbas yanzu bai da tarin iko mai tafe da karfin izza tunda har wata jaririya daga cikin yaran bil'adama tasha gabansa take wahal dashi tafi karfinsa tafi ƙarfin yaran fadar tasa, lallai suna da buƙatar sauya Sarki kada wata rana suna sake da baki ya jawo masifar da zatasa aci su da yaƙi a banza. (Gaba ɗaya abin da yan majalisar fadar ke rayawa a cikin zukatansu kenan akan Yah Malam).Ganin sun shigo cikin ɗakinsa sun yi zugum-zugum sai ransa ya sake ɓaci, zuciyarsa ta hasala nan take ya fara narkewa yana zama wani baƙin ruwa mai kama da tafasasshiyar dalma yana tururi da hayaƙi, ya nufosu , ai take suka fara zaro idanuwa waje domin sun san cewa duk wanda wannan ruwan ya taɓa shikenan shi angama da babinsa, domin toyasu yake ba tuyar arziki ba,cikin tashin hankali suka fara bashi haƙuri suna ja da baya,amma sai da ya mamaye wajen Aljanu hamsin sannan yayi tsiri sama ya zama gajimare ya ɓace bat.
Tunani take hawaye na zuba ta gefen idonta, tabbas akwai yiyuwar Innar tasu ta datse mata soyayya da wanda yanzu ne ta fara fahimtar yanda ƙaunarsa tabi jini da tsoka na jikinta, ta sake jawo wayar ta dubeta ko zata ga kiransa ko message nasa amma ba ko ɗaya da tagani, cikin kuka mai ɗaci tace "Ibnah karkai mun haka dan Allah, domin kaine mabuɗin jin daɗin lamarina tare da sanyaya rayuwata, haɗuwata da kai yasa na fara samun natsuwa da kwanciyar hankali, karda kasa na fara tunanin na zamanto ɗaya daga cikin waɗanda basuyi dace a soyayya ba,karka manta kaine wanda ko da yaushe kake jadadda mani yanda kake ƙaunata tare da son farin cikina, Ibnah idan har kace ka haƙura dani saboda Innata tabbas ka shiga rayuwata" kuka ya ƙwace mata mai karfi wanda sai da ƙannenta suka zagayeta suna tambayarta "mi take ma kuka? Cikin rashin tabbas dana sanin abin da zata furta masu ta share tambayarsu ta rungume su tana sake jin wani kukan mai karfi ya sake kucce mata, suma kukan kawai suka saka abin da ya jawo hankalin Inna Huraira kenan ta faɗo ɗakin har tana tuntuɓe " Na shiga ukuna ni Huraira kukan mi kuke ku kuma? To wallahi sai dai ubanku ya mace ba dai Huraira ba, ƙaryar banza ƙaryar wofi, duk nasan nufinku ai bama kamar yayar taku to wallahi sai Malam ya rigani mutuwa ƴan banza, kuna rufe mun baki ko sai jikinku ya gaya maku ne ? Ta rarumo kofi dake aje ta matso gabansu, tsit su kayi ba wanda ya sake ko tari, musamman Bilkisu da tasan ba ƙaramin aikin Innar tasu bane ta zane ta tsab ba. Cike da masifa tace maza ki tashi ki shirya ku tai makaranta na rasa zaman uwarwa kike a gidan nan da kika daina zuwa makarantar ja'ira Allah yasa su zaneki tas can. Ya juya tana masifar idan ta dawo ta iske su sai ta bugesu, harta koma ɗakinta tana masifa da tujara abin da yasa Malam ɗin fitowa daga ɗakinsa yayi mata magana "Haba Huraira daga samun sauƙinki zaki fara uzzura mata ko ? To wallahi ki kiyaye ba zan sake lamuntar abin da kike mata ba. Ai sai tayo waje kai buɗe tana jijjiga jikinta tana taɓa hannuwa tana cewa "Kasan Allah Malam da gaske nake kan yarinyar can sai munyi ruwan rashin arziki da kai ?To kama saurara kaji na rantse da Allah sai in bata kashi inga in zaka iya hanani" ya dubeta ya girgiza kai ya wuce yana "Allah ya baki lafiya Huraira lamarinki akwai firgicewa wallahi" ya leƙa ya iske har sun shirya fuskar Bilkisu kawai ya kalla yaga yanda taci kuka ga damuwa kwance akan fuskar yace "Yar albarka kiyi haƙuri da yanayin rayuwa wata rana sai labari, duk wanda ya ɗan ɗani ɗaci tabbas zai ɗan ɗani zuma kinji ? Kai ta ɗaga masa hawaye na shirin sake zubo mata ta kauda kanta, ta kama ƙannenta suka wuce islamiyar.
Huraira ta dubesu tace "Allah yasa a zaneki muga ta kukan ƙarya ja'ira kawai. Ita dai Bilkisu ta wuce tana jin jikinta sanyi ƙalau ba daɗi ko kaɗan a ranta. Tana zuwa islamiyar ta iske su Shema'u sunata tsara yanda saukarsu zata kasance nan da kwana biyar, ita dai tunda ta zauna ta saka kanta cikin cibiyoyin ta shikenan bata sake ɗagowa ba, su kuma baki ɗaya yanzu yan ajin mugun tsoron ganinta a damuwa suke dan ran nan a gabansu akai waja-waja da Malam Aminu (Ɗan-bahago)sannan sai da aka turo wasu narka-narkan sojoji suka zo suka yi kashedin duk wanda yayi mata kallon da bai gamsheta ba zai gane kurensa, dan haka ga tambaya suna san mata amma kowa na gudun karda ace shine yasata a ɓacin ran, ƙilu taja bau. Sai Shema'u da takasa natsuwa ta isa gunta ta ɗago kanta dan tambayarta abin da ke faruwa ta takura kanta,hawaye ta gani shar a fuskarta wadda sai da ta razana ganin kukan nata tamkar ya jima tana yinsa, cikin ruɗewa tace "Bilkisu ubanmi akai miki kike kuka haka? Salan kika wannan mahaukacin sojan yazo yayi mana dukan mahaukata ko ? Gaba ɗaya ajin yayi tsit wasu da dama sunji dama basu zo ba, domin basu manta yanda Malam Aminu (Ɗan-bahago) yayi ta amsar wuta ba anan har suman wucin gadi yayi akan idonsu, shine yau dan tsabar wulaƙanci tazo ta zauna cikinsu tana ta rusa kuka salan yazo yaci ubansu rana tsaka ? Nan take suka fara ficewa ɗaya bayan ɗaya kafin kace me, ajin ya zama daga Bilkisun sai Shema'u Yahaya dake ta tambayarta itama zuciyarta sai dukan uku-uku take, musamman data tuna randa Nasir ɗin yaje gidansu ya tabbatar mata da duk abin da ya samu Ibnarsa ta kiyayi kanta,har wata waya ya bata yace duk sanda wani abu ya taso tayi gaggawar kira za a zo garesu kai tsaye. Gama wannan tunanin ke da wuya tai wuf ta zuge jakarta sai ga wayar ta kuwa ɗauka ta fita tana kyarma ta fara ƙoƙarin kunna wayar hannu na rawa, yau komi ya samu Bilkisu haka ? Sai dai numbers biyu kawai tagani ɗaya ansa M, ɗayar ansa barrack, cikin rashin sanin wace zata kira ta danna ma M kira, ringin biyu aka ɗaga daga can aka ce "Miya faru da Ibnah ne Shema'u? Sai da hantar cikinta ta kaɗa jin muryai Nasir cikin wayar, cikin in ina tace "Daman tazo islamiya ne tana ta kuka taƙi gayamin abin da akai mata fuskarta har tayi kumburi..... Wata uwar tsawa ya daka mata.
"Stop Malama !
Ya kashe wayar baki ɗaya, jakwab ta zauna ta tallabe fuskarta tana jin koma miyasa tazo yau ? Ita kam wace ƙaddara ce tasa Nasir yasanta ma? Cikin ajin ta koma har zuwa lokacin Bilkisun kukanta kawai take ba ji ba gani abin takaici abin tausai ga Shema'un, ba zato ba tsammani sai jin dirin motoci sukai ƙofar ajin nasu, tare suka dubi ƙofar dan ganin suwaye kuma ? Malam Surajo na gaba da ganinsa kasan yana cikin zullumi da ruɗu,ya nuna masu Bilkisun yana cewa "Malama Bilkisu ki gaya masu ba wanda ya taɓa ki kaf makarantar nan dan Allah kinji ? Wani matsiyacin kuka ya kubce mata ta toshe bakinta kawai taci gaba da kukan, hakan yasa Sojojin suka ɗauka ko shine ya daketa dan haka suka fara ƙoƙarin sunkutarsa zuwa cikin motarsu, ganin hakan yasa Shema'u girgiza Bilkisun tana kuka "Baki kyauta ba Bilkisu kinyi zalunci kinso kanki akanme zaki saka a tafi da malam ? Mi yayi maki ? Sai lokacin Bilkisu ta ruga da gudu gun motarsu ta daka masu tsawa tana numfashi sama-sama tace bai mun komi ba, bani da lafiya ne . Sai lokacin suka ƙyalesa suka buƙaci Shema'u tazo su kai Bilkisun adubata asibiti, itakam Shema'u ba dan taji cewar bata da lafiya ba da saita ci mata haka kawai tazo ta ruɗasu a banza . Sai kuma ta kafe bata zuwa asibiti ita, ba yanda ba su yi ba amma tace ita sam ba inda zata je, ana cikin haka ne Malam Aminu yazo, tun daga nesa yake kallonta ya fahimci kuka take bai san lokacin da ya isa gunba ya fara jera mata tambayoyi kamar wanda ke cikin ruɗewa "Bilkisu lafiya kike kuka? Waya bugeki ne kike kuka ? Kina babba kina kuka ko baki lafiya ne ? Bilkisu mike damunki ne ? Gaba ɗaya sai mutanen gun suka koma kallonsa, hatta itama Bilkisun musamman yanda taga ya damu ainun har a idanunsa, kawai tasamu kanta da gaya masa bata lafiyane gida zata. "Ki zo muje na kaiki gidanto " abin mamaki wai yaro ya tsinci haƙori, ba Shema'u ba hatta sojojin sun saki baki suna kallonsa bama kamar waɗanda suka zanesa wancan ƙaron. Basuyi mamaki ba sai da suka ga Bilkisu ta haye mashin ɗinsa sun hau hanya .
Malam Sujaro shine yayi ma sojojin bayanin aikin Malam Aminu ne damƙa duk ɗalibin da bai lafiya gun iyayensa, dan haka kada su damu, sai lokacin Shema'u taji sanyi a ranta harta hango yanda zasu fara tamaula dashi ai, bayan tafiyarsu ne Malam Sujaro ke tambayar Shema'u abin da akaima Bilkisun take gaya masa iyakar saninta ita dai yace "Allah ya kyauta" ya koma office ɗinsa itama ta nufi gida dan ƴan ajin nasu duk sun tsorata sun arce tuni.
Tunda Inna ta kora su Bilkisu islamiya taci gaba da sababinta sai Malam ya fice zuwa kasuwa yabar mata gidan taji daɗin masifarta da tujara, ai kuwa ta ɗauko kujera ƴar tsugunno ta zauna taci gaba da tsine-tsinenta tana ƙara dagewa iyakar ƙarfinta, sam bata kula da wani ƙaton ɓera ba da yayi zugum yana kallonta yana kaɗa bindinsa, sai zuwa can ta lura da shi, ai kuwa ta yunƙura ta miƙe tana wani sababin kuma "Wallahi ɓeran nan anyi tantiri marar kunya, da ranar Allah ta ala zaka fito ƙiri-ƙiri kana kallona ƙuru-ƙuru? Barawon banza ashe kai ke cinye mun daddawa to yau zan maganinka ai matsiyacin banza. Ta sunkuci takalminta ta jefesa dashi, ko gezau saima ƙara kaɗa bindinsa yake irin bai damu ba ɗin nan, ai sai Huraira ta zabura ta nufesa tana cewa "Wannan balagaggen ɓeran ni zaima turjiya? Bari na take banza naga ubanda ya tsayama to, ai dai ba cizo kake ba balle ka razanani, tana isa ta ɗaga ƙafarta da nufin murjesa kawai taga ya koma ƙatuwar kada ta buɗe bakinta, haƙora zaƙo-zaƙo tana jiran saukar kafar Hurairar bakinta ta tamne ta cinye, wata uwar ƙara ta saka ta maƙale ƙafarta tana "Tsaya ƴar banza ba ɓera bane kada ce mai cizo, oh ni Huraira waya kawo mun kada cikin gidan nan dan mugunta ? To Allah ya isa wallahi ban yafe ba haka kawai aita mun aiken mugun abu. Ta fashe da kuka tana san sauke ƙafarta ƙasa, sai kuma ƙafar taƙi sauka ƙasan,cikin zaro idanuwa take kallon bakin kadar da ƙafarta ta fara ƙoƙarin tunano addu'ar aljanun ruwa ko shakka babu wannan kadar aljanar ruwa ce tazo a sigar kada, sai da ta jima kafin ta samu ta fara karanto addu'ar korar aljanun ruwa kamar haka....
"Allahumma minal ifiritul kulbi wa ƙoramati wa kwalbati anta ruwan dam, la la la cinye kafata kunta kada afara balle a gama lazinatul ɓace mun a gida .
Tunda ta fara karanto addu'ar sai kadar ta fara ƙanƙancewa harta koma kamar cinnaka wanda saika lurama da kyau zaka ganshi, ai Huraira na ganin kadar ta ɓace ma idonta sai ta buga ihu ta sauke ƙafarta ta fara kirari tana kambama kanta "Yo Allah na tuba daman ai ƙyale ku nake dan dai kuga kamar wata banza ce ni amma da ilimina ras tsaune cikin kaina, matsiyatan banza masu kawuna kamar na take kabewa, to daga yau ba aljanin da zan sake sauraramawa a cikin gidan mu zuba ni daku shege ka fasa. Tana ta masifa da cika baki kawai taji wani munafikin zafi ya ratsa kwanyar kanta yaba gaba ɗaya jikinta, kamar wadda akaima allura mai gubar zafi tabi jijiyoyin duka jikinta haka taji, ta kuwa daka tsalle ta fasa ihu tana "Allah ya isa wallahi ba zan taɓa yafewa ba tunda ba banza bace ba ni wallahi,dan kawai nayi addu'a kun toye shine zaku mun mugunta haka? Allah ya saka mun kuma addu'a yanzu na farata ta sake gyarawa ta buɗe murya iya kar ƙarfinta ta fara karanto addu'ar ...
"Altsine maku walkasheku wal azabaku wal masgeku wal toyeku wal haramta maku cutar Malama Huraira .
Malam Umaru da yaji sanda ta fara ihu tun ɗazun ya kwaso da gudu dan ganin ko lafiya, ya iske ta sai waɗannan surutan take sai abin ya bashi dariya ya tabbatar da cewa Huraira ta haukace, hauka mai wahalai magani dan haka sai ya juya da nufin fita daga cikin gidan, ita kuma Huraira sai ga kamar wani almajiri ne ya shigo yana kallonta sai ranta ya ɓaci ta sunkuci buta da ruwa da jefa masa tana cewa "Allah ya haɗaka dasu sai ka ji daɗin kallo ai ƴan banzan yaro.
Malam Umaru kawai ji yayi abu ya sauka da kyau a ƙeyarsa dan haka ya ida ficewa yana "Lallai Huraira tayi nisa gaba-gaba sai gidan mahaukata .
Yana ficewa da gudu sai Huraira taga wani wadan yaro na leƙowa yana mata gwalo, ta kuwa yi masa daƙuwa da hannuwa biyu tana barka masa zagi,ta uwa ta uba, dan ga dai zafin nan ya addabeta gashi yana tsokanarta sai abin yayi mata yawa, tana cikin zaginsa kawai taga ya shigo cikin gidan ya nufota yana taku guda yana ƙara gajarcewa yana tafiya yana gajarcewa sai gashi ya koma sak aljanin yaron nan dake takura mata, ai da gudu ta faɗa ɗakinta tana "Wallahi bazan tsayaba kawai ku cuceni. Ta afka ɗakinta ta rufe tana zare idanuwa kamar wadda taima Sarki ƙarya. Daidai nan Bilkisu ta shigo tana sallama ta shige ɗakinsu dan zuwa yanzu zazzaɓi ya rufe ta da gaske wanda shi kansa Malam Aminu sai da ya dinga jin zafin jikinta na dukansa, gaba ɗaya hankalinsa ya tashi yaji tamkar ya wuce da ita asibiti amma kuma tace bata so gida kawai take son ya kaita, dan haka ya kawo ta yaje ya samo mata magani dan wani irin tausayinta yake ji na ratsa gabban jikinsa baki ɗaya.
Tana shiga cikin ɗakin ta fiddo wayarta tana dubawa kawai ta lura ashema sim ɗin a rufe yake, har karkarwa take gun buɗewa tana jin tamkar tana buɗewa kiran Ibnah zai shigo mata,sai dai tsit dan haka ta latsa ta kira duk da tasan bata da kati amma dai haka nan take so ta furta abin da ke cikin zuciyarta ko daga ita sai wayar ne, dan haka cikin yanayin marar lafiya ta fara magana wayar na kunnenta bayan ta danna kiran.
"Ibnah kada ka zama ma'auni na auna jaririyar zuciyata da ba komi cikinta inba zallar ƙaunarka ba.
Ta ja numfashi mai tafe da ajiyar zuciya taci gaba.
"Ibnah kaine masoyina na farko na ƙarshe da nake fatan rayuwa dashi kaf tsawon rayuwata, dan Allah kada kace ka barni Ibnah ba zan jure ba Please kadawo gareni kada na faɗa mummunan yanayi dan Allah Ibnah karka barni .
Kuka ya kubce mata amma ta kasa daina maganar "Tunda kai mun nisa komi nawa ya ja baya, banda walwala banda farin ciki haka ban jin daɗin rayuwata domin kaine daman mai haskamun duhu da kalamanka tare da kulawarka gareni, Ibnah kazo gareni kaji ? Ta sake saka kuka mai tsuma zuciyar mai saurare.
Tunda kiran ya shigo ya ɗaga cikin sauri da nufin yi mata tambayoyi akan rufe wayar sai kuma yaji a yanayin da take magana, dan haka ya saka hansfree ya tsurama wayar ido yana kallonta, tare da godema Allah, domin tunda yake da Ibnah bata taɓa gaya masa yanda take jinsa a ranta ba sai yau, kenan rashinsa ne yasata ciwo da damuwa ? Bai san lokacin da yayi tsallen ihu ba ya hantsila ya sake hantsilawa yana jin cewa ba abin da zai hanasa zuwa gunta gobe domin ta sake maimaita masa kalaman nan .
Ita kuma a haka barcin wahala ya ɗauketa yana jin saukar numfashinta yasan tayi barci ya kashe wayar ya runtse ido yana murmushi, kamar ance buɗe idonka yaga wata ƙatuwar baƙar mage tana kallonsa ko ƙibtawa batayi . Ya tsira mata ido shima yana ƙare mata kallo kamar mai nazarin wani abu, itama magen kallon da yake mata take masa tamkar mutum.
To koya zata kaya ?
Mu haɗu a page nagaba.
managarciya