Malami Ya Rasu A Dakin Otel Yana Tsaka Da Yin Sharholiya Da Daliba A Jihar Kogi
Dr. Olabode Abimbola Ibikunle ɗaya daga cikin malaman da aka fi sani da "Tsauri" a Jami’ar Kogi dake Anyigba, ya rasu a cikin wani ɗaki na otel, a cewar rahotanni.
Dr. Ibikunle, wanda yake da aure da yara, an ce ya shiga otel ne kimanin kwana uku da suka wuce tare da wata kyakkyawar budurwa ‘yar Ebira, ɗaliba ‘yar ajin 200L a ɓangaren koyar da Social Studies.
An bayyana cewar malamin ya sha kayan ƙarfin maza da yawa kamar wanda zai buga wasan karshe na gasar Champions League.
Bisa ga labarin da ke yawo, an ce zagaye na farko ya tafi lafiya, amma kafin su fara zagaye na biyu, sai malamin ya fadi ya mutu nan take.
Lamarin ya tayar da hankali sosai a cikin jami’ar da kuma gari baki ɗaya, musamman ganin matsayin malamin da kuma yanayin rasuwarsa. Ana ci gaba da bincike a hukumance dangane da mutuwar tasa.
managarciya