Malaman Musulunci Sun Koka Kan Halin da Gwamnatin Tinubu Ta Jefa Al’umma

Malaman Musulunci Sun Koka Kan Halin da Gwamnatin Tinubu Ta Jefa Al’umma


Majalisar kolin shari’a da addinin musulunci watau NSCIA ta nuna takaicinta a kan halin da ake ciki bayan cire tallafin fetur. Vanguard ta ce sakataren NSCIA na kasa, Farfesa Is-haq Akintola a wani jawabi da a fitar, ya ce sun damu da yanayin al’umma a yau. 

Jawabin Farfesa Is-haq Akintola ya nuna mutane suna cikin mawuyacin halin tattalin arziki a sakamakon janye tallafi na fetur. 
"Majalisar (NSCIA) tana sane da cewa kalubalen da ake ciki sun yi yawa domin wadanda ke farfadowa daga fargabar ta’addanci da rashin tsaro sun ci karo da matsalolin tattalin arziki da har lamarin ya kai bukatun yau da gobe sun yi wa mafi yawan Musulmai wahala. A mafi yawan gidaje, ana neman yadda za a rayuwa ne yayin da adadin marasa hali yake cigaba da karuwa a cikin al’umma." 
Domin ganin an taimakawa marasa karfi, Is-haq Akintola yace suka fito da tsarin MESH wanda yake tallafawa jama’a tun a 2016. MESH ya taimakawa jama’a a bangaren ilmi, kiwon lafiya da walwala kuma har gobe a ba a gajiya ba ganin halin da jama’a ke ciki. NSCIA ta ce dole sai gwamnatocin tarayya da jihohi sun tashi tsaye wajen taimakawa marasa karfi bayan cire tallafin fetur. 
Rahoton ya ce kukan da majalisar take yi shi ne akwai jihohin da ake maida musulmai saniyar ware wajen rage radadin rayuwa. Akintola ya ce daga cikin jihohon da ake zargin an yi watsi da musulmai akwai jihar Filato.