Malaman makarantun firamare da ma'aikatan kananan hukumomi a jihar Taraba na ci gaba da kokawa kan rashin biyan albashi na tsawon watanni shida.
Wannan na zuwa ne a yayin da ake kara samun tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayan masarufi biyo bayan karuwar farashin dala a Najeriya.
Ma'aikatan na cewa sai sun sha bakar wuya suke iya rike kansu a halin da suke ciki, sakamakon rashin biyansu hakkokinsu da gwamnatin jihar Taraba ta yi.
Daya daga cikin dubban wadannan ma'aikatan ya ce sai an yi kamar za a magance musu wannan matsala, amma sai hannun agogo ya koma baya, maganar ta tsaya cik kamar dai su ba ma'aikata ba ne.
''Yanzu ta kai idan ka je karɓar bashi a matsayinka na malamin makaranta ma sai a hana ka idan aka gane cewa kai malami ne, domin an san cewa ba za ka iya biya ba, don ba ka da abun biyan'' inji shi.
Ita ma wata malama da BBC ta zanta da ita ta ce a halin da suke ciki suna nan suna ta kuka da 'ya'yansu don ba su da hatta abincin da za su ba su.
A cewarta ''Yanzu ko neman aure malami ya je yi baya samun mai aurarsa, sai dai ya nemi bazawara, domin sai ta rika ganin me zai ci me zai ba ta''.
Alhaji Abubakar Bawa shi ne mai bai wa gwamnan jihar Taraba shawara kan harkokin siyasa, kuma ya shaida wa BBC cewa ''Ba shakka ana biyansu hakkokinsu, amma ba zan iya ce maka ga inda aka tsaya ko watan da aka tsaya ba, amma ana ci gaba da biya''.
A halin yanzu dai malaman makarantun firamaren na zaman jiran gwamnatin jihar domin biyan su albashin watanni shida idan aka hada da na watan biyun shekarar 2016 da ba'a biya su ba, yayin da su kuwa ma'aikatan kananan hukumomi ke bin gwamnatin albashin watanni.
Gwamnatin jihar tana cikin gwamnatocin da ke wasa da biyan haƙoƙin ma'aikata.
Ta wace hanya ce ilmin jihar zai ɗaga a lokacin da Malamai ba su samun albashi, yaushe ne haujin zai samu tago mashi a wurin mutane a riƙa neman gurbi a wurin tun da an san duk wanda yake a can wahala ce kawai yake sha.