Majalisar dokokin Najeriya  ta tanadi daurin rai da rai ga masu safarar miyagun ƙwayoyi

Majalisar dokokin Najeriya  ta tanadi daurin rai da rai ga masu safarar miyagun ƙwayoyi

Majalisar dokokin Najeriya  ta tanadi daurin rai da rai ga masu safarar miyagun ƙwayoyi

Wannan shawarar ta biyo bayan amincewa da rahoton da majalisar dattawa da ta wakilai suka yi kan gyaran dokar NDLEA.

Da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin taron majalisar dattawa, Sanata Tahir Monguno, ya bayyana cewa gyaran yana neman sanya hukunci mai tsauri domin dakile ayyukan miyagun kwayoyi a Najeriya.

Harkar safarar miyagun ƙwayoyi lamari ne da yakamata gwamnatin Nijeriya ta ɗauki mataki mai tsauri kansa domin ganin an magance matsalolin da shan ƙwayoyin ke haifar wa.

Daga Abbakar Aleeyu Anache