Majalisar dokokin Kano ta aminta Abba Gida-Gida ya naɗa masu bashi shawara  20

Majalisar dokokin Kano ta aminta Abba Gida-Gida ya naɗa masu bashi shawara  20
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da bukatar Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ta neman ya nada masu ba shi shawara na musamman guda 20.
Kakakin Majalisar, Ismail Jibrin Falgore ne, ya karanta wasikar bukatar gwamnan a zauren majalisar a jiya Laraba.
Daga nan ne sai a ka tattauna wasikar kafin majalisar ta amince da bukatar.
Majalisar ta ɗage zaman ta zuwa ranar 19 ga watan Yuni, 2023 a wani kudiri da shugaban masu rinjaye, Honarabul Lawan Husaini (Dala) ya gabatar kuma ya samu goyon bayan shugaban marasa rinjaye, Labaran Abdul Madari (Warawa).
Wannan dai shi ne zama na farko d Majalisar Dokokin jihar ta 10 ta yi bayan rantsar da ita a ranar Talata.
Majalisar dai ta zabi Ismail Jibrin Falgore na jam’iyyar NNPP a matsayin Shugabanta