Home Rahoto Majalisar Dattawa ta amince da kudurin gyaran dokar zabe bayan zaman awanni...

Majalisar Dattawa ta amince da kudurin gyaran dokar zabe bayan zaman awanni biyar

8
0

Majalisar Dattawa a ranar Laraba ta amince da kudurin gyaran Dokar Zabe bayan shafe awanni biyar ana tattauna shi sashi-sashi.

Kudurin shi ne kaɗai abin da ke cikin jadawalin zaman majalisar bayan kammala zaman bankwana ga marigayi Okey Ezea, kuma kwamitin majalisar baki ɗaya ya amince da shi bayan nazari da kuma karɓar sassa 155 da ya ƙunsa.

‘Yan majalisar sun yi gyare-gyare ga wasu tanade-tanade, yayin da aka bar mafi yawan sassan kamar yadda aka gabatar da su tun farko.

Daya daga cikin gyare-gyaren ya rage wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) wa’adin sanar da zaɓe daga kwanaki 360 zuwa kwanaki 180.

Haka kuma Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da aika sakamakon zaɓe kai tsaye (real-time), tare da barin tanadin tura sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki kamar yadda Dokar Zabe ta 2002 ta tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here