Daga Babangida Bisallah, Minna.
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kasafin kudin matsakaicin zango na 2022-2024 (Medium Term Expenditure Framework - MTEF), kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar mata.
Amincewar ta biyo bayan nazari da doguwar muhawara akan rahoton kwamitocin majalisar da suka yi aiki akan bukatar ta shugaba Buhari.
Mai taimakawa shugaban majalisar dattawan akan aikin jarida Ezrel Tabiowo, FIMC, CMC, FCP, Fsca ne ya bayyana hakan a wata takardar manema labarai da ya fitar.
Majalisar ta amince da hasashen gwamnatin tarayya na samun harajin naira Tiriliyan 8.36 da kiyasin kashe Naira Tiriliyan 13.98 a shekarar 2022.
Majalisar ta amince da hasasahen samar da gangar danyen man fetur miliyan 2.23 a rana a cikin shekarun 2022, 2023 da 2024.
Haka nan ta amince da hasashen farashin mai na dalar Amurka 57 akan kowace gangar danyen man fetur; farashin dalar Amurka akan Naira 410 da hasashen habakar tattalin arziki da kashi 4.20 cikin 100 da amincewa da harhawar farashi da kashi 13 cikin dari.
Haka nan, majalisar ta amince da gibin kasafin kudi na Naira Tiriliyan 5.62, amincewa da ciwo sababbin basussuka na Naira Tiriliyan 4.89 da za'a ciwo daga cikin gida da kasashen waje bayan mika bukatar hakan ga majalisar dokoki ta tarayya.