Mai shagon abincin 30 ya yi murnar sauke Ministan Noman Nijeriya
Mai shagon abincin 30 ya yi murnar sauke Ministan Noman Nijeriya
Alhaji Haruna mai kwaki mutumin da ya buɗe gidan abincin naira 30 a jihar Kano ya baiyyana cewa yaji dadi mutuka da aka sauke Sabo Nanono daga Kan Kujerarsa ta minista.
A wata tataunawa da akayi dashi a Dala FM ya baiyyana cewa a yanzu haka kwanon garin kwaki yakai naira 900.
Ya kuma ƙara da cewa na ji daɗin sauke Ministan Gona, da shugaban kasa yayi saboda ban samu damar ganinshi ba, amma a lokacin baya mu tatauna.
Idan ba a manta ba i Alhaji Haruna shi ne mutumin da ya buɗe gidan abinci wanda yake yin haɗin garin kwaki na naira 30 domin nuna goyan bayansa ga maganar Sabo Nanono na cewa mutum zai ci ya koshi da naira 30 kacal a jihar Kano wanda maganar ta jawo cece kuce.
A jiya ne shugaba Buhari ya sauke Ministan saboda rashin taɓuka komai a aikin da aka ɗaura masa.
Bayan sauke ministocin biyu shugaban ƙasa ya bayyana cewa akwai da yawan ministocin da za a sauke nan gaba kaɗan domin kasa taɓuka komai.
managarciya