Mai baiwa gwamnan Sakkwato shawara kan hanyoyin karkara Malami Muhammad wanda aka fi sani da Bajare ya rabawa magoya bayan jam’iyar APC a jiha buhun shinkafa da taliya guda 1000 da kudi miliyan biyu domin sufurin kayan.
Malami Bajare wanda yake tsohon dan majalisar dokokin jiha ne ya ce ya yanke shawara raba abincin ga mutanen karamar hukumar Sakkwato ta Arewa domin ba da tashi gudunmuwa ga tallafawa magoya bayan jam’iyarsu.
“Jagorar wannan tafiyar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira gare mu duk wanda yake cikin gwamnati su yi iyakar nasu taimako ga al’ummar da suke tare da su, wannan ya karamin kwarin guiwa ba karami ba, na in tofa abin da Allah ya hore min.”
“In ka dubi abin da maigirma gwamna ke yi wurare daban-daban tun daga masu lalura ta musamman, mata da yara da limamai da Hakinmai da wurare daban-daban da ake bukatar taimako, ka ga yakamata in Gwamna ya yi gini ya yi filasta mu mukarabai sai mu yi fenti a kalla shi muke iya yi,” a cewarsa.
Ya ce sun baiwa rumfunan zabe 289 na mazabu 11 a karamar hukumakr Sakkwato ta Arewa, buhun shinkafa 500 da katon na taliya 500, duk rumfar da aka baiwa kayanta akwai kudin sufuri da za ta kai abin da ta karba zuwa gida.
Watan azumi akwai bukatar kara taimakawa mutane domin su samu sukuni da damar yin ibada ba wahala.






