Mahajjaciyar Nijeriya Ta Rasu A Filin Arfa
Allah ya yi wa wata mahajjaciyar Nijeriya, ƴar jihar Kaduna rasuwa a yau Juma'a a filin Arafat da ke birnin Makkah.
Rahotanni sun bayyana cewa, mahajjaciyar, mai suna Hasiya Aminu, daga Ƙaramar Hukumar Zariya a ta rasu ne a filin Arafat jim kaɗan bayan ta gama taimakawa wajen rabon abinci ga alhazai a tantinsu da ke filin na Arafa.
Da ya ke tabbatar da rasuwarta, muƙaddashin Daraktan Ayyuka na Hukumar Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, Abubakar Alhassan ya ce a safiyar yau marigayiyar na daga cikin alhazan da su ka je Jabbal Rahma (dutsen rahama) da ke filin Arfa.
Yace ta rasu a cikin tanti ba tare da wani ciwo ba.
managarciya