MAGEN KULU: LABARIN HIKAYA

MAGEN KULU: LABARIN HIKAYA
Hauwa'u Salisu (Haupha) 

Kofar fada ta cika da mutane kowa ka gani a zafafe yake wasu masu ƙarancin haƙuri sai zagi suke dannawa kamar tashin Maguzawa.

Taron mutanen ya haɗa da maza da mata ne yara da manya kowa kuma ransa a ɓace yake babu mai dariya ko fara'a a gun.

Mai gari da abin duniya ya isa yake dafe da kumatunsa ya sadda kansa ƙasa ya kasa ɗagowa ya kalli tarin jama'arsa da saura kaɗan su yi masa bore.

Wata matashiyar yarinya na gefe rungume da wata mage sai shafa bayan magen take hankalinta kwance ga alama bata da wata damuwa akan wannan zanga-zanga da mutanen garin ke yi tunda ita duk sanda ta shafi magen sai ta saki murmushi.

Wani matashine wanda ga alama ya fi sauran zafin kai ya ɗauki dutsi ya jefi yarinyar mai rungume da magen.

Dutsin kuwa ya sameta sai dai ko kallon inda jifar ta fito ba tai ba abin da take kawai ta cigaba da yi na shafa magenta tana mulmushi.

Mai gari ya rasa mafita ya kasa gane yadda zai ya fahimtar da mutane muhimmancin MAGEN KULU a garin nasu .

Duk da cewa itama MAGEN KULU abar tuhuma da zargi ce amma ta yaya za ai hakan? Kafin zuwan MAGEN KULU garin babu wadatar abinci haka yara ƙanana mutuwa su ke musamman jarirai ba su wuce ranar da aka haife su , sannan babu ruwa a duk rijiyar garin sai sun sha wahala sun je nesa da garin suke samo ruwa wanda akwai waɗanda da dama ƙishirwa ta halaka a garin.
Sai dai zuwan MAGEN KULU aka samu sauƙi komai ya zama tarihi kamar ba'a yi ba, amma kuma daga baya sai tsaffin garin ke mutuwa duk tsohon da zai mutu kalmar shi ta ƙarshe ita ce "MAGEN KULU!
Wannan kashe tsoffi shi ne abin da ya addabi rayuwarsu domin dai yanzu haka garin babu tsohon daya ba shekaru saba'in baya duk MAGEN KULU ta kashe su.

Babban tashin hankalin mutanen garin shi ne kada bayan ta kashe tsaffin ta koma kan dattawan garin masu sittin ko hamsin don haka suka yanke shawarar zuwa gun Mai gari ya ɗauki mataki akan MAGEN KULU ko kuwa su da kansu su ɗauki matakin kashe magen harma da mai magen idan ta nemi ba su matsala.

Mai gari ya saki kumatunsa ya ɗago ya dubi inda Kulu take zaune da magenta ya maida kansa kan jama'ar gari ya girgiza kansa ya miƙe tsaye yace "Kulu ta bi shi cikin gida zai magana da ita.
Kulu har zuwa yanzu ba wata damuwa a kan fuskarta abin da ke ƙara hassala mutane kenan game da ita har magen tata.

Mai gari ya dubi Kulu yace "Don girman Allah ki yi haƙuri ki janye alƙawarin dake tsakaninmu ki manta da sharaɗin da mu kai a yau a yanzu ki bar wannan gari Kulu tunda kinga mutane sun kasa haƙura da abin da ke faruwa."
Tunda Mai gari ke magana KULU bata kalleshi ba hankalinta na kan magenta sai shafar bayanta take .

Mai gari ya sake cewa, "Idan kin aminta ni nayi maki alƙawarin zan ba ki Shanu da Awaki tare da Kaji masu ɗinbin yawa waɗanda idan aka lissafa su za su kai yawan adadin sauran alƙawarin da ke tsakaninmu."

Kulu bata ce komai ba dai haka bata kalle shi ba.
Mai gari sai tunanin izza da mulkin dake gareshi ya motsa ya saurara ya ji yadda mutane ke ƙofar gida suna jiran yace su aiwatar don haka ya nuna Kulu da yatsa yace "Na fasa duk abin da nayi niyyar baki , idan kin isa ki hana a kashe MAGENKI KULU."

Ya fice ya dakawa mutane tsawa "Bance ku barta da rai ba tunda ta addabemu muma yau mu addabeta kowa ya ɗauki fansar jinin wanda ta kashe ma shi."

Sai a lokacin KULU ta ɗago kanta fuskarta ta sauya kumatunta sun lotse harshen ta ya fito waje kamar macijai hayaƙi na fita daga kowace kafa ta gashi a jikinta.
MAGEN KULU ma sai tai girgiza nan take ya koma wata mace marar kyan gani a cikin mummunar suffar da ta ninka ta Kulu muni .

Kofar shigowa ɗakin Kulu ta kalla sai kawai ta datse kanta da kanta.

Cikin muryar da tai kama da ta fatale tai ihu mai ƙarfi ta fara magana.

Can waje kuwa jin ihun yasa kowa ya razana wasu suka fara gudu wasu na taushe wasu hatta Mai gari sai da cikinsa ya yamutsa.

Kamar saukar aradu haka suka dinga jin ana magana wadda basu san daga inda take fitowa ba.

"MAGEN KULU ta fi ƙarfin ku taɓa ta kamar yadda kuka taɓa uwar kiwonta har kuka kasheta don kawai tana kiwon mage.
Ku sani duk wani bala'i da musiba Ku ne da kanku kuka kira abinku don haka dole ku amshi kowane irin hukunci.

Shin kun san wace ce MAGEN KULU kuwa? Ko kun san wace ce KULUN ?
Nasan ba za ku taɓa mantawa da HAUWA MAI ƘOSAI ba. Sannan ba za ku manta yadda ku kai rami kuka rufe su  tare da magenta ba. Nasan wasu ba su zo lokacinta ba amma an ba su labari don haka ku yi nazari sosai akan wace ce KULU da MAGE."

Nan da nan dattawan gun suka fara riƙe baki suna tafa hannuwa wasu kuwa hawaye ne ke zubowa daga idanunsu tabbas yanzu suka gane MAGEN KULU.

To wai wace ce MAGEN KULU ne ?
Wace ce HAUWA MAI KOSAI?
Me yasa mutanen gari suka rufeta da magenta?