Maganar Janyewa: Za Mu Tuntubi Kwankwaso A Lokacin Da Ya Dace----Shattima

Maganar Janyewa: Za Mu Tuntubi Kwankwaso A Lokacin Da Ya Dace----Shattima

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya magantu a kan yiwuwar hadakarsu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso gabannin zaben 2023. Daily Trust ta rahoto cewa Shettima ya bayyana cewa shi da kansa zai nemi Kwankwaso a daidai lokacin da ya kamata.

Tsohon gwamnan na jihar Borno wanda ke gabatar da jawabi a taron kungiyar limaman birnin tarayya Abuja, yana barkwanci ne da tsohon dan majalisar wakilai, Garba Ibrahim Muhammed, wanda ya wakilci Sanata Kwankwaso a taron. 
“Na sha alwashin ba zan taba muzanta Sanata Rabiu Kwankwaso ba har a gama zabe mai zuwa. Shi din shugaba ne nagari, kuma da izinin Allah, za mu zauna sannan mu fahimci junanmu a lokacin da ya dace nan kusa. “Wadanda ke shirin raba kan kasar nan ba za su cimma nasara ba, kuma saboda haka, ya zama dole mu lamunci junanmu sannan mu sadaukar da abubuwa.”