Mafi Karancin Albashi: NLC ta umarci mambobinta su fara yajin aiki a jihohi

Mafi Karancin Albashi: NLC ta umarci mambobinta su fara yajin aiki a jihohi

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya ce babu janye wa kan yajin aikin da aka shirya fara wa daga ranar 2 ga Disamba, 2024, a jihohin da ba a aiwatar da sabon mafi karancin albashi na Naira dubu saba'in ba.

Ajaero ya yi wannan bayani ne a yayin taron farko na manema labarai na Kungiyar 'Yan Jarida na Bangaren Kwadago (LACAN) tare da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya da shugabannin kwadago.

Ajaero ya kara haske kan umarnin da aka bai wa shugabannin jihohi da ba su aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu saba'in ba.

Dangane da Hukumar Kwadago ta Duniya (ILO), akwai bukatar gaggawa don haɗin gwiwa domin kawo karshen aikin yara da kuma hijirar kwadago ta barauniyar hanya.

Taron ya yi nazari kan sakamakon tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago a shekarar da ta gabata; nasarorin da aka samu da kuma hasashen gaba.