Ma’aikatar Shari’a Ta Tabbatar Da Goya Baya Ga Hukumar Bayar Da Gidajen Haya A Sakkwato
Ma’aikatar lamurran shari’a ta tabbatar da goya baya ga hukumar kula da bayar da gidajen haya a jihar Sakkwato don tsabtace haujin ga bara gurbi da tabbatar da gaskiya.
Kwamishinan ma’aikatar Barista Suleiman Usman(SAN) babban lauyan gwamnatin jiha ne ya sanar da hakan a lokacin da yake karbar shugaban hukumar Alhaji Namadina Abdulrahman(Talban Sokoto) da ya ziyarce shi a ofishinsa a ranar Talatar da ta gabata.
A takardar da babban darakta a hukumar Malam Usman Buhari Sani ya rabawa manema labarai ya ce shugaban ya yi wa kwamishina bayani kan aiyukkan hukumar da kaifin basirar da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yake da ita kan samar da hukumar da kuma yi mata gata ba abin da ta rasa a haujin aiki domin ganin an tsaftace matsalar harkokin gidajen haya a jihar Sakkwato.
A bayanin babban lauyan gwamnatin jiha ya duba dalilin samar da hukumar da goyon bayan da ma’aikatarsa za ta bayar yatabbatarwa shugaban hukumar da ayarinsa za su yi iyakar kokarinsu na tabbatar da nasarar aikin da aka daura masu.
Daga cikin ayarin shugaba akwai babban Mamba a hukumar Honarabul Bello Mai Lato Sanyinna, Honarabul Shehu Na Annabi, Honarabul Aminu Muh’d Mainiyo, Sai babban darakta a hukumar Mallam Usman Buhari Sani da daraktan mulki Mallam Ibrahim Yusuf.
managarciya