Ma'aikata Sun yi kira ga gwamnan Sakkwato ya biya su Kudin tallafi
Ma'aikatan gwamnatin jiha mambobin kungiyar kwadago ta kasa reshen Sakkwato sun yi kira ga gwamna Dakta Ahmad Aliyu Sokoto da ya biya kudin tallafi da gwamnatin tarayya ta umarci dukkanngwamnoni da baiwa ma'aikata tallafi don rage masu radadin halin da ake ciki na matsin rayuwa.
Mambobin da suka fito a ma'aikatun gwamnatin jiha sun tafi Gidan gwamnatin Sakkwato suna rare wakar 'wayyo yunwa a biya palliative' abin da ke nufin sako ne suke aikawa gwamnan jiha ganin bai waiwayi batun ba har yanzu.
Kungiyar kwadago reshen Sakkwato sun bi takwarorinsu na sauran jihohi a Talata wurin zanga-zangar da suka shirya don fadakar da gwamnatin tarayya halin da ake ciki, da zimmar kawar da hauhawar farashi a cikin al'umma.
Sakkwato na cikin jihohin da ma'aikata ba su amfana da tallafin rage radadin wahalar da aka shiga tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi ba.
Dubban ma'aikatan sun fito zanga-zangar ne domin sanarda shugabanni halin da kasa take ciki da bukatar ɗaukar matakin gaggawa.
Shugaban kungiyar Alhaji Abdullahi Jangul ya godewa mambobinsa da hadin kan da suka bayar na fitowa kan kwatar 'yancin 'yan kasa.
Ya ba su tabbacin cigaba da fafutika har a samar da cigaba da yanani Mai kyau a kasar Nijeriya.
managarciya