Ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya sun yi gargaɗin cewa farashin man fetur (PMS) a Najeriya na iya kaiwa kusan naira 2,000 kan kowace lita, yayin da diesel kuma zai iya kusantar naira 3,000, idan rikicin da ke faruwa a gabas ta tsakiya ya ci gaba.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Billy Gillis-Harry, ya ce rikicin da ya haɗa da Israel, Iran da kuma Amurka na ƙara dagula farashin mai a duniya.
Ya bayyana cewa kafin rikicin, ana sayar da fetur kusan N774 kan lita, amma yanzu ya haura N1,000, yayin da diesel ya tashi daga kusan N950 zuwa sama da N1,400 kan lita.
Gillis-Harry ya buƙaci NNPCL da ta ƙarfafa tace mai a cikin gida, tare da gaggauta farfaɗo da matatun gwamnati kamar matatar Port Harcourt da Warri domin rage dogaro da kasuwar mai ta duniya.
Wannan lamarin ya nuna Matatar man fetur ta Dangote ba ta samar da cikakken saukin da ake bukata ba, tare da bayyanar cewa har yanzu Nijeriya na dogara da man da ake shigowa da shi kenan daga kasashen waje.
Wannan lamarin ya kara nuna cire tallafin mai da gwamnati ta yi kuskure ne babba hakan zai cigaba da sanya rayuwar mutane cikin kunci da rashin tabbas.






