Lamido Ya Yi Ta'aziya Ga Mutanen Goronyo Kan Harin 'Yan Bindiga

Lamido Ya Yi Ta'aziya Ga Mutanen Goronyo Kan Harin 'Yan Bindiga

 

Alhaji Ibrahim Lamido dan takarar dan majalisar dattijai a yankin Sakkwato ta Gabas a zaben 2023 karkashin jam'iyar APC,  ya yi wa mutanen karamar hukumar Goronyo da yankin Sakkwato ta tagabas ta'aziya kan mummunan harin da 'yan bindiga suka kai a ranar Laraba data gabata.

Harin da aka kai a kauyukkan Bare da Kojiyo ya yi sanadin salwantar rayukka shidda tare da barnata kayan abinci da gidaje da dama.
Lamido ya nuna takaicinsa sosai kan wannan aikin ta'adanci da aka yi ba laifin zaune ko tsaye a zo a kashe mutane ba da hakki ba.
Ibrahim Lamido ya yi addu'ar Allah ya gafartawa wadan da suka rasa rayukkansu, wadan da suka yi hasara Allah ya mayar musu da mafificin alherinsa.
A zantawarsa da wakilinmu ya yi kira ga hukumomin da ke kula da lamarin tsaro su kara tashi tsaye tare da kawo wasu sabbin dubaru domin magance matsalar tsaro dake addabar yankin Sakkwato ta Gabas.