Lafiya Jari: Amfanin Ganye Gwanda Ga Mata

Lafiya Jari: Amfanin Ganye Gwanda Ga Mata

Ganyar gwanda na kumshe da sinadiran lipid, calcium, iron, bit C, bit B6, folate, Thiamine, magnesium, phosphorus, potassium, sodium, zinc, Bit A, bitamin E, Bitamin D, D2, D3, Niacin da sauransu.

Ganyen gwanda a binciken wassu masanan kiwon lafiya da sukayi ( Dr. Nam Dang da Dr. Gajawik A) suka ce yana dauke da sinadarin lycopene sidari ce wacce take kashe kwayar cutar daji.

Molecular Nutrition and Food Research tayi bincike kuma ta gano ganyar gwanda na dauke da sinadiran papain da chymopapian masu rage kumburi a sassa da dama na jikin dan’adam.

A sakamakon arziki na wannan sunadarai, idan ana dafa ganyar gwanda ana shan ruwan ta da izinin Allah zai magance wadannan matsaloli:

1- Ganyar gwanda na habaka garkuwar jikin dan’adam.

2- Yana cire kasala tare da karfafa gabobi da lakar jikin dan Adam.

3- Yana saukaka narkewar abinci da kuma tace shi daga cututtuka.

4- Yana inganta lafiyar zuciya tare da ba ta kariyar cututtuka.

5- Yana hana kamuwa da ciwon sukari ta hanyar daidaiton sinadarin Insulin a jikin dan Adam.

6- Ganyen gwanda yana taimaka wajen kashe  tsutsotsin ciki.

7- Ganyen gwanda na narkar da sinadiran cholesterol da yawansu a jiki illa ne.

8- Yana azurta jikin dan Adam da wadataccen jini.

 

9- Yana hana kumburin jiki haka kuma yana kara lafiyar hantar dan Adam.

10- Ganyen gwanda na wanke kazamta da wani abu mai cutarwa da ya yi laulayi a kan babbar hanji.

GARGADI:kada mai juna biyu ta yi amfani da ganyen gwanda domin tana motsa nakuda, haka kuma kada ta wuce kofi guda biyu a rana, domin yawan shan ruwan ganyen na kawo hajijiya(jiri) da gani dishi dishi.

Duk abin da ya shafi kiyon lafiya a rika bincikar masana da likitoci domin kare lafiyar jiki daga fadawa cikin matsaloli nay au da kullum da suka shafi lafiya.