Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin komawa jam’iyyar ADC a ranar Litinin mai zuwa.
Majiyoyi sun shaida cewa wannan sauyin sheƙa ya biyo bayan makonni na shawarwari tsakanin Kwankwaso, ƙungiyarsa ta Kwankwasiyya da shugabannin jam’iyyar ADC.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya yi jerin ganawa da manyan jiga-jigan ADC da sauran ‘yan adawa a ‘yan makonnin nan.
A makon da ya gabata, ya gana da shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki a Kano a matsayin wani ɓangare na ci gaba da tattaunawa.
Haka kuma, ya tattauna da wasu manyan ‘yan siyasa, ciki har da Sakataren Ƙasa na ADC, Rauf Aregbesola; ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi; gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde; da Sanatan Bayelsa ta Yamma, Seriake Dickson.
Rahotanni sun ce wannan mataki na daga cikin yunƙurin sake fasalin haɗin gwiwar ‘yan adawa gabanin babban zaɓen 2027, domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan da aka samu rabuwar alaka tsakanin Kwankwaso da tsohon yaronsa a siyasa kuma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Gwamna Yusuf, wanda ake kallonsa a matsayin ɗan siyasar da Kwankwaso ya raina da ƙungiyar Kwankwasiyya, ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC tare da wasu ‘yan majalisa da masu riƙe da muƙaman gwamnati.
Sai dai Kwankwaso ya nuna rashin amincewa da wannan mataki, inda ya nisanta kansa da shi tare da bayyana hakan a matsayin cin amana.




