Home Labarai Kwankwaso ya bukaci daukar matakin gaggawa kan ‘yan ta’adda bayan harin Maiduguri

Kwankwaso ya bukaci daukar matakin gaggawa kan ‘yan ta’adda bayan harin Maiduguri

2
0

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna matukar alhini kan hare-haren kunar bakin wake da suka faru a birnin Maiduguri, inda aka ruwaito yayi ajalin mutane 23 tare da jikkatar sama da 100.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya bayyana harin a matsayin mummunan lamari da ya kawo cikas ga zaman lafiyar da aka fara samu a jihar Borno a shekarun baya.

A cewarsa, sabbin hare-haren na nuna yiwuwar sake dawowar ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, abin da ya ce ba za a amince da shi ba.

Tsohon gwamnan ya kuma bukaci gwamnatin Nijeriya da na jihohi da su dauki matakan gaggawa domin magance matsalar tsaro, tare da bai wa jami’an tsaro dukkan kayan aiki da goyon bayan da suke bukata domin yakar ‘yan ta’adda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here