Home Siyasa Kwankwaso: Gwamna Yusuf zai yi nadamar ficewa daga NNPP

Kwankwaso: Gwamna Yusuf zai yi nadamar ficewa daga NNPP

4
0

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran jam’iyyar NNPP, ya ce Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da makusantansa za su yi nadamar ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, inda ya ce ficewar gwamnan ta ba mutane da dama mamaki, har ma da shi kansa, yana mai cewa dukkan dalilan da aka bayar na sauya sheƙa abubuwa ne da za a iya warwarewa ta hanyar tattaunawa.

Gwamna Yusuf ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a ranar 26 ga Janairu, 2026, bayan ya sanar da murabus dinsa daga NNPP, yana mai cewa ya ɗauki matakin ne bisa duba alkiblar siyasar Nijeriya da muradin kawo ci gaba ga al’ummar Kano.

Sai dai Kwankwaso ya yi watsi da zargin rikici a cikin NNPP, yana mai jaddada cewa jam’iyyar na cikin kwanciyar hankali.

Ya kuma ce yadda tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya karɓi Gwamna Yusuf a APC alama ce cewa gwamnan zai fuskanci ƙalubalen siyasa.

Kwankwaso ya ƙara da cewa Kano har yanzu na NNPP ce, kuma motsin Kwankwasiyya na nan da ƙarfinsa, yana mai tabbatar da cewa Gwamna Yusuf, ko da bai koma jam’iyyar ba, zai yi nadamar barinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here