Home Labarai Kwankwasiyya ta yi watsi da Zargin tsattsauran ra’ayi da ƴan majalisar Amurka...

Kwankwasiyya ta yi watsi da Zargin tsattsauran ra’ayi da ƴan majalisar Amurka suka yi wa Kwankwaso

7
0

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta yi watsi da zargin da ake yi wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a cikin wani kudiri da ke gaban Majalisar Dokokin Amurka, tana mai cewa zarge-zargen marasa tushe ne kuma na yaudara.

A cikin kudirin mai taken Nigeria Religious Freedom and Accountability Act 2026 (HR 7457), an ambaci sunan Kwankwaso dangane da zarge-zargen take hakkin ‘yancin addini.

Sai dai a wata sanarwa da kakakin ƙungiyar, Dr. Habibu Sale Mohammed, ya fitar a Kano, ya ce tarihin rayuwa da hidimar Kwankwaso ba su nuna wani laifi na tsattsauran ra’ayi ko cin zarafin addini ba.

Ƙungiyar ta bayyana cewa tsarin Shari’a da aka kafa a wasu jihohin Arewa yana ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma ba Kano kaɗai ba ce ta aiwatar da shi.

Ta kuma buƙaci Majalisar Dokokin Amurka da ta cire sunan Kwankwaso daga cikin kudirin, tana mai zargin cewa wasu na ƙoƙarin amfani da batun domin cimma manufofin siyasa.

Kwankwasiyya ta jaddada cewa Kwankwaso ɗan kishin ƙasa ne wanda ya tsaya kan adalci, haɗin kai da zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here