Kwamitin Tunibu: Ya gana da Sarkuna da Malamman Addinai a Zamfara

Kwamitin Tunibu: Ya gana da Sarkuna da Malamman Addinai a Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim.

Masu iya magana na cewa,Mai Zurfin Ido da wuri ya ke Fara kuka ,Wannan ne ya sanya , Kwamitin yakin Zaben Dan takara Shugaban Kasa na Jamiyyar APC ,Ahmad Bula Tunubu , Karkashin jagorancin Shugaban Kamfendin na Jihar Zamfara,Sanata Kabiru Marafa ya gana da Sarakuna da Malaman Addini sun amshi  Koken su dan sanin yadda za a'amagance su .

 Sanata Kabiru Marafa ne ya tabbatar da  haka alokacin da ya ke amsa tanbayoyin manema labarai a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

  " Marafa ya Kara da cewa, Kwamitin sa ya Fara tuntubar Shugabannin Al'umma,Sarakuna ,Malaman Addini da Kungiyoyi dan gano bakin zaren da zasu daure dan samun nasarar cin Zaben Shekara ta 2023.

Kuma Wannan shine zai bamu dama ta ganin hakarmu ta cimma ruwa, wajan samun nasarar Zaben Dan takarar mu na Shugaban Kasa , Ahmad Bula Tinubu.inji Sanata Marafa.

"Sanata Marafa ya Kuma tabbatar da cewa,sunsan an bata wa Mutane Kuma zamu basu hakori ,akan Dan takarar mu su gwada shi su gani da yardar Allah zaiba mara da kunya.

Kuma duk kan koken  dan muka amsa na Sarakuna da Malaman Addini da Kungiyoyi , zamuyi masu Karatun tanatsu dan ganin mun sharema Al'umma hawayen da ke zuba a idanun su.inji Sanata Kabiru Marafa.

Kuma yanzu haka Kwamitin ya bude Ofisoshin sa ya Jiha,da Yankunan Mazabar Dan Majailisar Dattawa .dan soma yakin kafen din Ahmad Bula Tinubu.