Kwamitin bincike da gwamnatin Sakkwato ta kafa ya gargaɗi tsohon mataimakin gwamna Alhaji Manir Muhammad Dan’iya a karo na karshe da ya bayyana a gabanta a zaman da za ta sake yi 22 ga watan Mayun 2024.
Haka ma kwamitin ya tura irin wannan gargadin ga tsohon babban daraktan kamfen jam’iyar PDP a zaben 2023 Alhaji Yusuf Suleiman Ɗan Amar Sokoto.
A cewar kwamitin dukkan su biyu akwai bayanin da ake so su yi a gaban kwamitin kan wani Memo 007 da ke gaban kwamitin.
Lauya Dan’iya, Barista Nuhu Adamu ya nemi a sanya masu wata rana abin da shugaban MU’AZU Pindiga ya aminta da hakan.
Ya umarci ‘yan sanda su lika takardar gayyata a jikin ginar Dan’amar Sokoto in har ba a same shi gida ba.




