Kwalara ta kashe mutane sama da 20 a Kano
A jihar Kano, ana fargabar mutum fiye da 20 sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar kwalara a wasu ƙauyuka.
Bayanai na cewa lamarin ya auku ne sanadiyyar gurɓacewar ruwa sakamakon ambaliyar ruwa kuma kawo yanzu mutum fiye da ɗari ne suka kamu da cutar a ƙauyuka biyu, inda wasu ke karɓar magani.
Bayanan da BBC ta tattaro daga kauyukan Mikiya da Ballagaza cikin karamar hukumar Gabasawa a jihar Kano na cewa mutanen garin sun fara ganin waɗanda suka harbu da cutar amai da gudawar ne bayan da aka yi mamakon ruwan sama tun a makon jiya.
Baya ga larurar amai da gudawar dai yanzu haka hukumomi a Kanon, sun ce suna bin diddigi da bincike bayan mutuwar fiye da mutum 40 sakamakon kamuwa da cutar mashaƙo akasari ƙananan yara.