Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Gamayyar qungiyoyin matasa da mata ne (YOCOPA) a qarqashin jam'iyyar APC, daga qananan hukumomi 17 dake faxin jihar wanda suka gudanar da gangami tare da jerin-gwano, domin nuna cikakken goyon bayan su ga Gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni, a babban birnin jihar, Damaturu a ranar Talata.
Bugu da qari, gagarumin taron ya qunshi shugabanin matasan tare da na mata a kowane mataki, kana kuma ya samu halartar qusoshin gwamnatin jihar da na jam'iyyar APC a kowane mataki a jihar- waxanda suka haxa da Gwamnan jihar, Kakakin Majalisar Dokokin jihar, shugabanin jam'iyyar APC da Sakataren gwamnati da sauran su.
A jawabin Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, wanda mataimakin sa ya wakilta a taron; Alhaji Idi Barde Gubana, a taron wanda ya gudana a babban filin wasa na 27 August dake Damaturu; ya yaba wa matasan bisa jajircewa, haxin kai tare da fatan ganin matasan sun yi gagarumin shirin tunkarar zaven 2023 mai zuwa.
A hannu guda kuma, Gwamnan ya gargaxi matasan da su ci gaba da haxa kai kuma su guji duk wani abin da zai jawo tashin hankali a jihar a lokacin yaqin neman zabe da zave.
Hon. Barde ya ce Gwamna Buni mutum ne mai kishin al’amuran matasa, kuma ya cika dukkan alkawuran da ya xauka a lokacin yaqin neman zave ta hanyar baiwa matasa muhimmanci tare da naxa su muqamai a faxin jihar.
Gwamna Buni ya yaba wa qungiyoyin matasa da mata, waxanda suka shirya wannan gagarumin gangamin tare da nuna cikakken goyon bayan da suke baiwa gwamnatinsa.
A jawabin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyya ta xaya (Zone A), Alhaji Mustapha Gaidam tare da mai baiwa Gwamna shawara na musamman kan harkokin siyasa da majalisar dokoki, Hon. Aji Yerima Bularafa sun jaddada buqatar ci gaba da wayar da kan jama’a kan sabon tsarin zave da INEC ta bullo da shi.
Har wala yau sun buqaci gamayyar qungiyoyin matasa da mata dake qarqashin jam'iyyar APC a jihar su guji saka kansu cikin ayyukan da za su kawo wa jam’iyyar cikas tare da qara zage dantse wajen jawo hankalin al'ummar jihar su zavi APC a kowane mataki.
A nashi jawabin, shugaban gamayyar qungiyoyin, Hon. Babagana Alh. Modu (Bature Goniri), ya bayyana cewa manufar taron ita ce nuna amincewar matasa da mata tare da jaddada goyon bayansu ga takarar Gwamna Mai Mala Buni da mataimakinsa Hon. Idi Barde da sauran dukan yan takarar jam’iyyar APC, kuma taro ne na dukkanin qungiyoyin jam'iyyar APC a jihar.
Shima da yake tofa albarkacin bakinsa, Ko'odinatan Hukumar Sake Raya Arewa Maso Gabas (NEDC) a jihar Yobe, Dr. Ali Ibrahim Abbas ya ce matasa a jihar za su ci gaba da nuna godiya da alfahari da gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni kan yadda yake nuna cikakkiyar kulawa wajen haxa kai tare da qoqari wajen inganta rayuwar matasa don ci gaban al’ummar jihar Yobe baki xaya.
Yayin da aqarshe mataimakin gwamnan ya karvi xaruruwan 'ya'yan jam'iyyar PDP waxanda suka sauya sheqa zuwa APC daga qananan hukumomin Goniri, Gujba da Nayi-nawa a Damaturu.
Hoto: Mataimakin Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Idi Barde Gubana a lokacin gangamin matasan, a Damaturu.