Kungiyar Lauyoyi Ta Yi Allah-wadai da shigo da jami'an tsaron Kano

Kungiyar Lauyoyi Ta Yi Allah-wadai da shigo da jami'an tsaron Kano
 

Kungiyar NBA ta lauyoyi ta reshen jihar Kano ta yi Allah-wadai da yadda aka shigo da jami’an tsaro a rikicin masarauta. 

Kungiyar lauyoyin na Kano suna ganin wannan yunkuri da sunan neman tabbatar da hukuncin kotun tarayya ya sabawa doka.
Daily Nigerian ta rahoto cewa neman tursasa bin umarnin kotu da taimakon sojoji da ‘yan sanda ba shi ne abin da ya kamata ba. 
Sanarwar lauyoyin ta fito ne ta bakin shugaban NBA na reshen na Kano, Sagir Gezawa. Sagir Gezawa ya bayyana cewa akwai hanyoyin doka da ake bi domin tabbatar da cewa an yi biyayya ga hukuncin da alkali ya yi. 
"A matsayinmu na lauyoyi, mun damu sosai da abubuwan da suke faruwa ta hanyoyi da-dama 
Majalisar dokoki ta na da hurumin yin doka, kuma da zarar an amince da ita, gwamna yana da hakkin ratabba hannu a dokar. Da zarar gwamna ya sa hannu, ta zama doka kuma dole wadanda abin ya shafa suyi biyayya kuma dole kotu ta tabbatar da ita." - Kungiyar NBA
Ana da labari wata kotun tarayya ta ba da umarni a dakata da sauke Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan da aka kirkiro a 2019.
Gwamnatin jihar Kano tayi fatali da wannan hukunci, har Abba Kabir Yusuf ya yi barazanar kai karar alkalin a wajen nada sabon sarki da ya yi.