Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kamar Yadda Ta Tsara

Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kamar Yadda Ta Tsara

 

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi fatali da rahotannin da ke cewa tana duba yiwuwar dakatar da zanga-zangar gama-gari da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan, ranar Laraba, 2 ga watan Agustan 2023.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a shafinta na Twitter da yammacin ranar Talata, 1 ga watan Agusta, ƙungiyar tace ba ta sake duba matsayarta ba ko dakatar da zanga-zangar kamar yadda aka rahoto tunda farko. 

A cewar sanarwar wacce shugaban ƙungiyar na ƙasa, Joe Ajaero ya rattaɓawa hannu, ƙungiyar ta haƙiƙance cewa har yanzu ba ta sauya zani ba kan buƙatun da ta ke neman a biya mata.
Ƙungiyar ta haƙiƙance cewa za ta gudanar da zanga-zangar a gobe Laraba, kamar yadda ta shirya. Emma Ugbaja, sakataren ƙungiyar ƙwadagon, bayan kammala zama da kwamitin gwamnatin tarayya, ya ce matakan da Shugaba Tinubu ya fara ɗauka abun a yaba ne amma sun yi kaɗan.
Daga nan ya yi nuni da cewa ƙungiyar ƙwadagon da ƙungiyar ma'aikata za su tattauna da mambobinsu domin cimma matsaya kan matakin da za su ɗauka zuwa ƙarshen ranar Talata kafin a fara zanga-zangar ranar Laraba.