KUNGIYAR BUNKASA AIKIN JARIDA TA IPC TA HORAR DA 'YANJARIDU KAN HARKAR TSARON INTERNET

KUNGIYAR BUNKASA AIKIN JARIDA TA IPC TA HORAR DA 'YANJARIDU KAN HARKAR TSARON INTERNET

DAGA ALI RABIU ALI.

Kungiyar Bunkasa aikin 'yanjaridu ta International Press Center LPC, ta horas da 'yanjaridu harkokin tsaro da yadda zasu killace ayyukansu na yanar gizo-gizo dan kaucewa masu kutse.

An gudanar da horon ne a Kano Wanda kungiyar ta IPC ta hada da tallafin gidauniyar 'yaraduwa da MacAuther foundation a ranakun 5 da 6 na yulin shekarar 2022.
Taron Wanda aka gudanar da Shi na kwanaki biyu, an zakulo masu aikin jarida da kafafen Radio da Talabijin da sauran Jaridu ciki har da jaridar internet ta zumahausa.
Da yake gabatar da takardar sa daya daga cikin masu horaswar, Dr. Nura Ibrahim ya ja hankalin 'yanjarida dasu tabbata suna ajiye bayanan su da ayyukan su a gurare daban daban Kamar su computer da flash da hard disk da sauran su domin kaucewa bacewar bayanai.
Ya kuma bada shawarar saka mukullin rufewa da budewa na email ko ku Wana gurin da ake ajiye bayanai domin tabbatar da tsaro daga kaucewa masu fasa kaurin internet.
Dr. Rukayyah Aliyu Bello, itama daya ce daga cikin malaman horas da 'Yanjaridun, ta ce da akwai kalubale dayawa da yake samun danjarida musamman a lokacin da yake neman bayanan bin kwakkwafi Wanda ake Kira investigative reporting ko kuma journalism a turance.
Dan haka Dakta Rukayyah ta ce yazama wajibi Dan jarida ya fara kula da lafiyar sa da rayuwar sa kafin gudanar da aikin rahoton bin kwakkwafi duba da irin hadarin da yake tattare da aikin.
Tace akwai lokuta da dama da ake kaiwa yanjarida musamman masu aikin bin kwakkafin rahoto hari, wasu ma har rasa rayuwar su sukeyi.
Zumahausa ta rawaito cewa Mahalarta taron sun bayyana irin halin da suka tsinci kan su a yayin ayyukan su daban daban a fadin kasar nan.
Sun kuma yi Kira ga gwamnati da ta Yi kokari wajen tabbatarwa bawa 'yanjaridu kariya a lokacin da suke gudanar da ayyukan su na jarida.