Kungiyar ACF ta bukaci a gudanar da bincike kan harin sojoji kan mutan-gari a Sokoto

Kungiyar ACF ta bukaci a gudanar da bincike kan harin sojoji kan mutan-gari a Sokoto

Kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa ACF ta yi Allah wadai da harin bam da sojoji suka kai wa al’ummar Silame a Jihar Sakoto, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da jikkatar wasu da dama.

Kungiyar ta kuma yi kira da a gudanar da bincike kan harin tare da bai wa wadanda abin ya shafa diyya yadda ya kamata.

Sakataren Yada Labarai na ACF na Kasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, a Kaduna, ya bayyana harin da ya faru a ranar Kirsimeti a matsayin “kuskure daya da ya yi yawa.”

“Mun shiga damuwa da alhini kan abin da ya faru a Silame, wanda ya zama daya daga cikin abubuwan da suke faruwa da  yawa a kasar nan.

"Ba wani al’amari ne da aka ware ba, domin muna da tunanin wasu hare-hare makamantan wannan da suka faru a al’ummar Tudun Biri a Jihar Kaduna kimanin shekara guda da ta gabata, da kuma a baya a jihohin Adamawa da Nasarawa, wadanda ke da mummunan kididdigar wadanda suka rasa rayukansu,” in ji shi.

Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan martanin sojoji game da harin, musamman bayanin wani kakakinsu da ya ce an kai harin ne kan wani wurin da aka tsara.

ACF ta bayyana wannan martanin a matsayin “rashin tausayi” tare da yin kira da a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.