"Ku Yi Hattara": Gwamnatin Sokoto Ta Ankarar da Jama'a kan Sabuwar Barazanar 'Yan Ta'adda

"Ku Yi Hattara": Gwamnatin Sokoto Ta Ankarar da Jama'a kan Sabuwar Barazanar 'Yan Ta'adda

 
Gwamnatin jiihar Sokoto ta gargadi mazauna yankin gabashin jihar da su kasance masu taka tsantsan game da ƴan ta’addan da ke guduwa. 
Gwamnatin ta yi wannan tunatarwar ne biyo bayan ci gaba da kai hare-hare da sojoji suke yi kan ƴan ta’adda a gabashin Sokoto da kewaye. 
Jaridar Daily Trust ta ce gargaɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), wanda kuma aka fi sani da Sadaukin Gwadabawa, ya sanyawa hannu.
A cewar sanarwar, haɗin gwiwar aikin jami'an tsaro da gwamnatin jihar ta ɗauki nauyinsa a yankin ya samu nasarori sosai. 
An bayyana cewa nasarorin da jami'an tsaron suke samu sun ƙara dagula lamurran ƴan ta’addan da ke yankin waɗanda suka shiga halin ƙaƙani-kayi. 
A yayin samamen an gano maboyar ƴan ta’adda da dama tare da lalata su, yayin da aka kashe wasu daga cikinsu. 
Hakazalika, jami'an tsaron sun ceto ɗaruruwan mutanen da aka yi garkuwa da su a yayin wannan aiki da suke ci gaba da gudanarwa. 
Sanarwar ta yi kira ga mazauna yankin su kasance masu lura tare da sanar da hukumomi duk wani motsi da basu yarda da shi ba a yankunansu. 
"Ƴayin da jami’an tsaro ke ƙara matsa lamba kan ƴan ta’adda, suna tserewa zuwa wasu yankuna tare da waɗanda suka samu raunuka daga cikin su." 
"Muna wayar da kan jama’a don jawo hankalinsu kan su yi taka tsantsan, saboda wasu daga cikin ƴan ta’addan na iya yin basaja domin neman mafaka a ƙauyuka ko neman a duba lafiyarsu a asibitocin karkara." - Kanal Ahmed Usman 
Gwamnati ta ƙarfafa gwiwar mazauna yankunan kan su riƙa kai rahoton duk wani motsi da ba su amince da shi ba ga hukumomin tsaro.