'Ku Agaza Mana': Iyaye Sun Koka Yayin da 'Yan Bindiga Suka Sace Kananan Yara Sama da 30 a Jihar Katsina

'Ku Agaza Mana': Iyaye Sun Koka Yayin da 'Yan Bindiga Suka Sace Kananan Yara Sama da 30 a Jihar Katsina

 

Iyaye a garuruwan karamar hukumar Faskari, inda yan bindiga suka sace yara 39 yayin da suke tsaka da aiki a gona sun roki gwamnati da ta ceto yaran daga hannun wadanda suka sace su. Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigar sun mamaye wata gona a ranar Lahadi inda suka yi awon gaba da yara fiye da 40 da suka hada da maza da mata yayin da suke tsaka da aiki. 

Wata majiya a garin Mairuwa, inda harin yafi muni ta ce yan bindigar sun mamaye gonar sannan suka fara harbi kan mai uwa da wahabi kafin suka sace ma'aikatan. 
Ya ce wakilin mai gonar ya tara yaran bayan ya biya yan bindigar harajin naira miliyan 1, inda ya kara da cewar yawancin manyan da ke aiki a gonar sun yi nasarar tserewa a yayin harin. 
"Sun bukaci naira miliyan 3 daga mai gonar kafin ya iya girbe amfanin gonarsa, ya basu naira miliyan 1 don rage hanya sannan ya yanke shawarar fara aiki kafin ya cika sauran kudin, amma abun bakin ciki yan bindigar basu yarda da hakan ba. A kauyenmu, Mairuwa kadai muna da mutum 33 cikin wadanda aka sace harda yan mata da suka isa aure," in ji majiyar. 
Wani mazaunin garin Mairuwa wanda ya tabbatar da wannan labari ya ce: "Mai gonar dan Funtua ne, amma wakilinsa na zama a nan kauyen Mairuwa. Yanzu da mike magana, yan bindigar sun yi amfani da wayar daya daga cikin mutanen da abun ya ritsa da su inda suka bukaci a biya kudin fansa naira miliyan 30. "Sun ce sun farmaki gonar ne don sace mai gonar ko wakilinsa amma saboda basu samu kowannensu ba sai suka yanke shawarar garkuwa da wadanda ke masu aiki."